Connect with us

Fasaha

2020: Ga dukkan alamu Shekara ce dake jaddada muhimmancin amfani da Fasaha

Published

on

Ga dukkan alamu Shekara ce dake jaddada muhimmancin amfani da Fasaha

2020: Ga dukkan alamu Shekara ce dake jaddada muhimmancin amfani da Fasaha.

Wannan batu ya taso ne bisa la’akari da yadda komai ya sauya salo a wannan duniya musamman a cikin wannan shekarar 2020. Tun farkon duniya al’amuran fasaha suke ta sauya fasalin yadda ake gudanar da aiyuka a fanoni daban-daban. Kusan kowacce shekara tana da irin nata cigaban da take zuwa da shi. Fasaha ta sauya abubuwa masu yawan gaske, ta samar da cigaba, ta samar da saukin yadda ake gudanar da aiyuka, ta samar da aiyukan yi masu yawan gaske cikin fadin duniya, ta samar da kusanci a tsakanin mutane daga sassan duniya mabambanta. Dan haka ilimin fasaha har ma da kimiyya suka zamo ginshikai wajan sarrafa dukkan al’amura yau da kullum a duniya.

Ga kadan daga cikin abubuwan da shekarar 2020 ke kara jaddada muhimmancin amfanin su ga duniya baki daya.

  • Harkokin Kasuwanci a Intanet (e-commerce); kasancewar annoba ta hana cudanya tsakanin al’umma domin dakile yaduwar cutar covid-19, dole ne al’umma suyi kasuwanci domin cigaba da rayuwa kamar yadda aka saba. Dan haka fasaha tana taka muhimmiyar rawa a fannin kasuwancin duniya baki daya.
  • Amfani da jirgi maras matuki domin isar da sakonni (drone delivery); ko dayake ana amfani da wannan fasaha wajan isar da sakonni ta hanyar amfani da jirgi mara matuki a wasu kasashe tuntuni. Akwai yiwuwar za’a kara kaimi wajan amfani da wannan fasaha, duba da yadda cudanya tsakanin jama’a take zama hadari a wannan shekara.
  • Amfani da tsarin zamani wajan biyan kudi (digital contactless payments); wannan tsari shima ba sabo bane domin tuntuni ana amfani da hanyoyin zamani wajan biyan kudin cinikayya a kowanne bigire. Hanyoyin kuwa sune:- Amfani da Kati (Credit Card, Visa Card, Master card, Verve Card), Amfani da na’urori kamar wayoyin zamani (smartphone) da Kwamfutoci, da kuma amfani da hanyoyin biyan kudi ta intanet kamar paypal, google pay, da sauran manhajoji na bankuna daban-daban. A wannan shekara amfani da wannan fasaha ya zamo tilas domin cigaban al’amuran yau da kullum.
  • Tattaunawa tare da ganin juna kai tsaye (video conferencing); duba da yadda aka shelanta zaman gida ga Ma’aikata, ‘Yan Kasuwa, Makarantu da sauran wuraren da Jama’a ke cudanya, domin kaucewa kamuwa da annobar coronavirus. Wannan tsari shine lamba daya wajan tafiyar da dukkanin wadancan misalai da na bayyana a sama ba tare da an cudanya da juna ba. Fasaha ce da ke bada damar tattaunawa tsakanin al’umma dake sassa daban-daban kai tsaye kuma ana kallon hotunan juna ta fuskokin na’urori kuma ana amfani da sadarwar intanet mai sauri da kuma cikakken tsaro.
  • Sanya abubuwa a jiki domin kulawa da lafiyar dan Adam (wearable health monitors); Fasaha ta samar da abubuwan da al’umma ke amfani da su domin kulawa da lafiyar su akai akai ba tare da sunje wajan likita ba. Akwai Zobe, Sarka, Agogo da sauran su wadanda aka tsara su musamman domin kula da lafiyar jikin dan Adam. Suna nuna karfin bugawar jini, Yanayin Numfashi, Zafin jiki, da sauran sassan jiki. Wannan fasaha tana taimakawa al’umma wajan kula da kan su, ba tare da taimakon likita ba.
  • Sabon Tsarin kere-kere na fasaha zamani (3D manufacturing); wannan hanya mafi sauki wajan kera abubuwa musmman ta hanyar amfani da na’urar kwamfuta wajan tsarawa da kuma fitar da shi a zahirance a tsarin siffa mai kusurwa 3. Yanada sauki idan aka kwatantashi da abubuwanda aka kera a babbar masana’anta. Wannan fasah zata bada damar kera abubuwa kamar na roba ko kwali ko soso kuma ayi amfani dashi. Ingancin abubuwan da aka kera ta wannan fasaha ya dogara da darajar na’urori da kuma kayan aikin da aka siya, ma’ana tsadar su wajan mallaka. Akwai na’ura wadda tayi kama da wadda ake hadawa da kwamfuta domin buga rubutu a takarda (Printer) ana kiranta 3D Printer. Da ita ake amfani. Domin karin bayani akan wannan tsari sai a ziyar ci Shafin —>
  • Hanyar kiran waya mafi saukin Caji (voice mobile applications); Shi ma wannan tsari ne na fasaha da ake amfani da shi a na’urori domin yin kira ba tare da credit ba. Ana amfani da tsarin sadarwar intanet wajan aiwatar da hakan. Kuma ana kiran tsarin da suna VoIP wato Voice over IP. Kuma akwai manhajoji masu yawa da ake amfani da su domin cin gajiyar wannan fasaha. Misali ana amfani Skype, WhatsApp, Telegram, Imo, Facebook Messenger, Wechat da sauran su.
  • Tsarin koyo da koyarwa a Zamanance (online learning & teaching); Kusan wannan fasaha ta zamo tilas a wannan lokaci, amma itama ba sabuwar fasaha bace amma dole ta kara fadada a wannan yanayi na kowa ya kasance a gida domin kubuta daga cutar corona virus. Kuma hanya ce mafi sauki wajan gudanar da al’amura daga gida ba tare da anyi cudanya ta zahiri ba.

Kadan kenan daga cikin abubuwan fasaha da shekarar 2020 ke jadda amfanin su ga duniya baki daya.