32 C
Kano
Saturday, November 28, 2020

ROM

ROM shima daya ne daga cikin sassan adana aiyukan kwamfuta. wanda shi kuma ya sha bamban da RAM, saboda shi ma’adana ce ta dindindin. Na’uara tana iya karanta abubuwan dake cikin ROM amma baza’aiya gogewa ba. Kamar CD ko DVD na kallo a gida da sauran su.

Sannan a cikin kwamfuta da dange-dangenta akwai nau’in ROM dake da matukar muhimmanci wanda yake taka muhimmiyar rawa wajan tafiyarwa da kuma kulawa da dukkan yadda mu’amala take kasancewa tsakanin hardware da software, tundaga farkon fara aiki har zuwa lokacin da za’a kashe ta.

Shi wannan ROM ana iya sauya wani bangare daga cikinsa, kuma ana kiransa CMOS CHIP. Wanda an kerashi ne akn PROM. Wato wanda ake iya sauya wani bangare daga cikinsa.

error: Alert: Content is protected !!