Connect with us

Labari

Kamfanin Apple ya Cika Shekara 44 da kafuwa.

Published

on

A Yau ne kamfanin Apple ya Cika Shekara 44 da kafuwa

Kamfanin Apple ya Cika Shekara 44 da kafuwa.

Shahararren kamfanin Apple wanda ya yi shuhura wajan kerawa ko samar da na’urori masu inaganci da nagarta, da saurin sarrafa aiki da kuma daraja ko tsada wajan mallakarsu.

An kaddamar da kamfanin Apple dake Amurka a 1 ga watan Aprilun shekarar 1976. Kamfanin yanada yawan ma’aikata kimanin dubu dari da hamsin da bakwai (157,000). Kamfanin ya bayyana kudin shiga da ya samar tun kafuwar sa zuwa karshen shekarar da ta gabata (2019) kimanin Dala Billion Dari Biyu Da Sittin da Dari da Saba’in da Hudu ($260,174 Billion).

Manyana mutane sun fi amfani da kayan wannan kamfani duba da tsarin su da kuma yadda sukayi shuhura a duniya fiye da sauran samfuran wayoyi na wasu kamfanoni.

Kayan kamfanin Apple sunyi zarra, domin har zuwa wannan lokaci ba a sami damar satar fasahar su ba wajan kera wayoyi irin nasu. Kamfanin Apple ya kera wayoyi samfurin iPhones, iPad da suran su…

Wayoyin Kamfanin Apple basu fiye fuskantar matsaloli kamar yadda sauran wayoyin zamani ke fuskanta. Kuma Mafi yawancin manhajojin su ba kyauta ba ne.

Nan gaba zamu tattauna akan wayoyin Apple…