Connect with us

Fasaha

Abubuwa 15 da yakamata kowa ya sani game da fasahar 5G

Published

on

Fasahar-5G

Abubuwa 15 da yakamata kowa ya sani game da fasahar 5G

A karshe-karshen shekarar da ta gabata ne ake ta hasashen yadda Fasahaar 5G zata bazu a duniya baki daya kamar yadda ake tsammanin fara aiki dashi a cikin wannan shekara ta 2020. Saboda haka shafin duniyar fasaha online yaga dacewar sanar da Jama’a abubuwa 15 domin a kara samun kyakkyawar fahimta baki daya.

 1. 5G na nufin karni na 5 a daga cikin karnonin fasahar sadarwa (5th Generation Cellular Network). Wanda kuma shine kan gaba, mafi saurin sadarwa fiye da kowacce fasahar da ake amfani dasu kafin ta.
 2. Fasahar sadarwa ta 5G zata kawo gagarumin cigaba a fagen sadarwa ta duniya. Daga cikinsu akwai guda 3 da muka zakulo kamar; (1) Babban bututu (larger channel) domin tsananta saurin hanyoyin sadarwa, (2) Dakile jinkiri wajan aikawa da isar da sako akan lokaci (3) Bada damar kulla alaakar sadarwa tsakanain na’urori masu yawa a lokaci guda.
 3. Hakika tsarin fasahar 5G ta bambanta da tsarin fasahar 4G, haka zalika girman mamayar (Coverage area) tururin sadarwar su ba daya bane.
 4. Fasahar 5G tana amfani da tsarin tururin sadarwa (wave) guda 3; akwai karamar shimfida (low-band) wanda yayi daidai da matakin fasahar 4G, sannan matsakaici (Mid-band) wadda ta dara 4G, da kuma babba ko mafi girma (High-band) wanda shine sabo da ake jira ya watsu cikin duniya a fara amfani dashi.
 5. Fasahar 5G itace ta farko da zata kawo sauyin wayar hannu (Mobile Phone) ta yi amfani da dukkanin tsarin hanyoyin sadarwa (all-band) gaba daya kuma a lokaci guda. Sabanin yadda a wayoyin yanzu suna iya amfani da tsari daya (1-band) ne, hakan yasa tilas mutum ya zabi gudaya da zaiyi amfani dashi.
 6. Saurin sadarwar 5G zai rubanya na 4G sau dari (x100) wanda hakan zai bada damar sauke (download) cikakken faifan bidiyo (full movie) a cikin ‘yan dakikoki.
 7. Ana ta raderadin cewar 5G zai iya haifar da illa ga lafiyar Jama’a duba da karfin sadarwarsa da kuma tururin mayen karfe da yake amfani dashi. Amma dai har zuwa yanzu babu wani bayanin illa ko cuta da masana harkar lafiya suka furta. An sa ran bashi da matsala kamar na baya.
 8. Fasahar 5G zatayi fice fiye da sauran na baya, wajan sarrafa na’urori ma bambanta ta fuskar girma, tsarin kira da kuma irin fasahar su domin basu damar amfana da sadarwa amfi sauri daidai da karfinta.
 9. Tsarin Intanet ta 5G zata doke intanet na 4G ta fuskar saurin sadarwa kamar yadda ake amfani dashi a yanzu. Kuma zai kasance mai sauki ga kamfanoni sadarwa wajan isar da tsarin intanet mai sauri ga Jama’a ba tareda sunyi hake-haken ramuka da binne-binnen manyan igiyoyin sadarwa (optic fiber) a lungu da sako ba.
 10. Har zuwa wannan lokacin kasuwancin Fasahar 5G a duniya bai girma ba. Domin Fasaha ce da zata kawo babban sauyi ta fuskoki daban-daban kama daga; Nuna hotuna taratar, kallon faifan bidiyo kaitsaye (Fast Video Streaming) ba tareda kakkatsewa ba. Kuma zata inganta fasahar masana’antu wajan kere-keren a baben hawa marasa matuka, da kuma fahimtar junansu akan hanya lokacin zurga zurga.
 11. 5G na da karfin kulla alaakar sadarwa tsakanin na’urori masu yawan gaske a lokaci guda, haka kuma 5G zai inganta mu’amala da manyan wayoyin hannu na zamani (smart phones) da kuma inagnta aikin maganadisu (sensors).
 12. Zuwan wannan sabon tsarin sadarwa ta 5G, zai kawo sababbin sauye-sauye ta fuskar kirkire-kirkiren na’urori masu basira da hikima (Artifitial Intelligence).
 13. 5G zai zamo na farko a duniya wajan sauya tsarin gudanar da harkokin manyan kamfanoni wadanda aka karkasa su a sassan duniya. Kuma kowa zai iya gudanar da aiyukansa daga ko ina ko a halin tafiye-tafiye kama daga; Jirgin Sama, Jirgin kasa da motoci da sauran su, cikin matsanancin sauri.
 14. Babban hasashe akan Fasahar 5G shine kawo babban sauyi ta fuskar mu’amalar manyan wayoyin hannu wajan aikata abubuwan mamaki da fikirar tsara aiyuka kamar a mafarki (virtual reality), wadanda suka shallake tunanin ‘yan Adam. Hakan zai kara bunkasa damammakin kasuwanci a fadin duniya.
 15. Tabbas, ga dukkan sabon al’amarin da ya bijiro a duniya, akwai yiwuwar kashe makudan kudade wajan sauya (upgarde) karikitai (gadgets) ko sassan na’urori (Hardwares) domin suyi daidai da bukatar sabuwar fasaha. Dan haka tun daga yanzu yakamata kowa ya fara tanadin shiga tsarin amfani da Fasahar 5G tun kafin tazo.

Hakika, wannan fasaha ta 5G tana kunshe da tanade-tanade da kuma bukatar yin tanadi tun kafin tabbatuwar sa. Kuma za’a sami bullar sababbin aiyukan yi a fadin duniya baki daya.

Muhadu a rubutu na gaba…

Continue Reading