Connect with us

Wayoyin Zamani

Abubuwan da ke haddasa sankamewar waya

Published

on

sankamewar-wayoyin -hannu-samfurin-smartphone

Abubuwan da ke haddasa sankamewar waya.

A lokuta da dama na kan sami tambayoyi daga masu amfani da wayoyi samfurin smartphone, wato wayoyin zamani, akan wata matsala da take addabar su a lokacin da suke sarrafa wayoyin domin biyan bukatun su.

Wannan matsala itace sankamewar waya (freezing) a lokacin da aka kunna ta ko ana tsaka da aiki da ita. Akwai dalilai da suke haddasa wannan matsala. Wasu daga tsarin wayoyin ne, wasu kuma daga masu sarrafa wayoyin ne. Akwai kamfanoni da dama da suke kera ire-iren wadannan wayoyi musamman samfurin Android. Wasun su sunyi shuhura wajan samar da manyan wayoyi masu sauri (speed) da kuma manyan rumbuna (large memory) domin adanawa ko ajiye kayayyaki. Wasu kuma sai a hankali. babu yabo babu fallasa. Koda yake IYA KUDIN KA IYA SHAGALIN KA haka na’urorin fasaha suke  a kasuwa dama sauran al’amura.

Abubuwan dubawa kafin siyan sabuwar waya ko Kwamfuta;

  • Darajar Saurin Masarrafi (CPU Speed): Saurin masarrafi a waya har ma da kwamfuta na taka muhimmiyar rawa wajan tafiyar da kowanne irin aiki da akeyi cikin sauri. Akasin haka kan haddasa nawa ko nauyi wajan sarrafa aiki da na’ura. Kasancewar sa jigo yayin sarrafa aiki.
  • Girman rumbun aiki (Amount of RAM): Haka shima rumbun aiki wanada dukkan aiyukan da’akeyi a cikinsa akeyi. Wadatarsa na taka muhimmiyar rawa wajan bawa na’ura damar sarrafa aiyuka masu yawa a lokaci guda. Kankantar sa tana dakile duk wani sauri da masarrafi ke dashi, da kuma hana budewar manhajoji da yawa a lokaci guda domin gudanar da aiyuka. Hakan babban dalili ne da kan haddasa sankamewar na’ura.
  • Sabuntawar Manhaja (Android/iOS Version): kamfanoni kera na’urori kan sabunta manhajar sarrafawa a lokuta daban-daban, wanda hakan ya bayyana darajar manhaja daga matakin farko zuwa na gaba. Wanda hakan yana inganta aiyukan na’ura har da karin karfi akan matakan tsaro. Tsohuwar manhaja takan kasance cinkushe da matsaloli dazara an kirkiro sabuwa. Hakan yakan tilasta masu amfani da wayoyi ko kwamfutoci damar sabuntawa domin samun gudanar da aiyuka cikin nisahadi. Sabuntawa ko daga darajar manhaja yana inganta tsarin tafiya na’urori, akasin hakan kuma yana haddasa rashin sauri da rashin gudanar da aiki daidai ga wasu manhajojin dake kan na’urar koma suki yin aiki gaba daya.
  • Girman Rumbun ajiya (Amount of Storage Capacity): Shima wannan rumbun ajiya ko adana kaya na taka muhimmiyar rawa wajan daukar kaya masu yawa ba tareda ya cinkushe da wuri ba. Idan kuma ya kasance karami akan sami jinkiri wajan sarrafa na’ura. A lokacin da na’uara ta rasa sararin dana kaya wannan dalili ya kan haddasa anuyi wajan sarrafa aiki.
  • Cutar Na’ura (Virus da dagin su): Lallai wannan ma babban al’amari ne da kan haddasa sankamewar na’ura. Domin da zarar cutar virus ta kama waya ko kwamfuta, takan haddasa matsaloli masu yawa. Cutar Virus tana sauya akalar duk wata manhaja ta hanayar hana ta aiki ko yin wani abu na daban sabanin yadda aka tsarata. Kuma cutar tana mamaye duk wata ma’adana dake na’urar, hakan yana haddasa sankamewar na’ura a lokacin da cutar tayi mamaya.

Matakan da ya kamata adauka domin magance wannan matsala ta sankamewa

  1. Cire duk wata manhajar da aka dade ba a aiki da ita, musamman idan akwai karan cin girman sassan da na ambata a baya.
  2. Saka Manhajar kariya wato Anti-Virus
  3. Sabunta manhajojin dake na’ura akai-akai
  4. Yin garambawul (Maintenance) ta hanyar share burbushin kayan aiki (Temporary Files) kasancewa akwai manhajoji da aka tsara su domin gudanar da hakan (Utilities).
  5. Da sauran su…

Da fatan Allah ya amfanar damu gaba daya!!!

Continue Reading