Connect with us

Kwamfuta

Abubuwan da ya kamata ayi la’akari dasu kafin siyan Kwamfuta.

Published

on

Abubuwa masu muhimmanci da ya kamata ayi la'akari dasu kafin siyan Kwamfuta

Abubuwa masu muhimmanci da ya kamata ayi la’akari dasu kafin siyan Kwamfuta.

Wannan batu ya taso ne bisa yawan tamabayoyi da jama’a suke aikowa akan neman sanin yadda mutum zai tantance irin Kwamfutar da ta dace ya siya domin gudanar da aiyukan yau da kullum. Sanin muhimman abubuwa kafin mutum ya mallaki na’ura yanada amfani kwarai da gaske. Abubuwan suna da yawa amma zanyi bayani akan wadanda suka muhimmanci.

Jama’a da dama sukanyi la’akari da kyalkyalin kwamfuta ko sunan kamfanin da ya kera kwamfuta, duk da cewa sunan kamfani yana da matukar tasiri musmman kamfanin da yayi shuhuwa wajan samar da nagartattun na’urori. To amma wasu lokutan akan yi zaben tumun dare. kaga mutum kwana biyu da siyan kwamfuta, yazo yana neman siyar da ita domin ya sayi wadda zata dace da bukatar sa. Kuma dole ne ya yi asara wajan sake siyar da ita.

Idan mutum bashi da ilimin fahimtar ingancin na’urori, to yanada kyau ya tuntubi wanda ya sani musamman dalibai masu nazari a fannin ilimin kwamfuta. A matakin farko yanada kyau mutum ya tantance bukatar irin kwamfutar da ta dace ya siya, ta girke (Desktop) ko ta yawo (Laptop). na biyun su kuma karfin aljihu (Budget), na ukun su kuma ga su kamar haka;

Masarrafi (Processor): shi ne a matsayin kwakwalwar na’urar kwamfuta, kuma ana bayyana saurinsa wajan sarrafa aiki a matakin GigaHertz (GHz). Yanada kyau a sayi kwamfuta wadda take mafi saurin sarrafa aiki, amma kuma ta kanyi tsada sosai saboda saurinta shi ne darajarta. Shi yasa a wannan matakin yake da kayu mutum yayi nazari akan bukatarsa ta mallakar kwamfuta da kuma irin aikin da zai yi da ita. Idan ya kasance aikin da zaiyi da ita bai wuce rubuce-rubucen ba, irin na aikin ofis ko amakacin haka, baya bukatar siyan kwamfuta sama da 1Ghz na msarrafi. Idan kuma ya kasance aikin sa mai nauyi ne kamar aikin sarrafa Hotuna, Bidiyo masu nauyi da inganci sosai, to anan akwai bukatar babban masarrafi kamar 1.5Ghz zuwa 2.5Ghz ko 3.0Ghz.

Rumubn Aiki (RAM ko Memory): Kusan duk saurin masarrafi (CPU) a kwamfuta ya dogara ne da girman rumbun aiki. Dukkan aiyukan da akeyi da na’urar Kwamfuta a cikin wannan rumbu ake gudanar da shi. Kuma ana auna adadin girmansa a tsarin ma’auni na Gigabyte (GB). Saboda haka a kowacce irin bukata ana so ya kasance mai girma akalla 4Gigabyte.

Rumbun Ajiya (Hard Disk Drive): Wannan shi ne wajan da ake adana dukkan aiyuka, manhajojin aiki, manhajara sarrafa na’ura ma acikin sa ta ke da sauran abubuwan da ake iya adanawa a kwamfuta. Shi ma girmansa yana taka muhimmiyar rawa wajan siyan kwamfuta. A shekarar 2014 aka samar da sabon samfurin rumbu ajiya na musamman mai suna Solid state. Ya bambanta da na asali kamar haka; Saurin aiki da kuma kasancewar sa babu tarkace masu motsi a cikinsa kamar na asali. Amma kuma yanada matukar tsada sosai. Anan mutum zai iya siyan kamar 320GB, 500GB, 650GB, 750GB ko 1Terrabyte. 

Injin Sarrafa Hoto (Graphics Card): Wannan ma yanada matukar fa’ida, saboda shi ne jigo wajan sarrafawa da tace hoto da bidiyo a kwamfuta domin bada ingantaccen hoto a manunar kwamfuta (Display). haka kuma akwai manhajoji wadanda aikinsu ya dogara ga ingancin hoto ko bidiyo domin samun cikakken sakamakon aikin su Misali HD Videos da Advance Games. An fi samun na musamman masu inganci fiye da wadanda suka zo a cikin kwamfuta. Sai dai tasada sosai kuma an hada su da kwamfuta ta hanyar USB ko kuma Hanyar karawa kwamfuta sassa na musamman (expansion slot).

Manhajar sarrafawa (Operating System): Kusan kaso tamanin (80%) na kwamfutoci da ake aiki dasu  aduniya suna amfani da manhajar sarrafa kwamfuta na kamfanin Microsoft, wato Windows. Wasu lokutan akan siyar da kwamfuta da windows akan ta, haka zalika akn siyar da su babu windows akan su. Sai dai mutum ya zabi irin wanda yake so domin a saka masa ko ya ska da kansa. A halin yanzu windows mafi dacewa akan kwamfuta shine windows 10 ko kuma windows 8.1.

Wadannan abubuwa sune suka fi dacewa da ayi la’akari da su a duk lokacin da aka tashi siyan kwamfuta.

Mu hadu da ku a ‘Abubuwan da ya kamata ayi la’akari da su kafin a sayi Wayoyi ‘Yar Zamani (SmartPhones)’