Connect with us

Wayoyin Zamani

Abubuwan dake haddasa zafin Waya da hanyoyin magance hakan

Published

on

abubuwan dake haddasa zafin waya

Abubuwan dake haddasa zafin Waya da hanyoyin magance hakan

Wannan al’amari ne da ake yawan aiko da tambaya akansa. Hakan yasa nayi wannan yunkuri domin a sami damar magance wannan matsala. Akwai dalilai masu yawa da suke haddasa wannan matsala ta zafin waya, wanda har takan haifar da konewar wasu sassa na wayar ko ita kanta wayar ta kone kurmus!

Bisa tsari na’urori sukan yi dumi lokacin da ake gudanar da aiki dasu. Amma wasu lokutan dumin yakan zamo zafi, ko tsananin zafin da a wasu lokutan wayoyin sukan sanar ko nuna alamar tsanin zafin dake tattare da su wanda ka iya jawo babbar asara. Ga kadan daga cikin dalilai da suke haddasa tsananin zafi yayin sarrafa waya;

 1. Sarrafa waya a wajan da yanayin sadarwa (Network) ba shi da karfi sosai. A duk lokacin da mutum ya kasance a wajan da ake da rashin karfin sadarwa, wayar ta kanyi amfani da dukkan karfin ta domin jawo sabis, wanda hakan yana jawo zukewar batir da haddasa zafin waya.
 2. Bude manhajoji masu yawa a lokaci guda. Sarrafa manhaja fiye da ka’ida kan jawo massarafi (CPU) yin aikin da ya wuce ka’ida. Hakan yana haddasa karuwar zafin waya.
 3. Amfani da tsarin sadarwa na wi-fi na tsahon lokaci. Amfani da tsarin wireless wanda ya hada da wi-fi, bluetooth da sauran su.. fiye da kima. Wannan ma yana haddasa daukar zafi.
 4. Sarrafa waya a cikin yanayin zafi. A lokacin tsananin zafi na yanayi, zafin na’urori yakan karu har ma ya zarce kima saboda dumamar yanayi. ko kuma a jiye ta a hasken rana.
 5. Amfani da tsarin kymara (Camera) mai darajar inganci na karshe (Hi resolution). A wannan lokaci na kwalliya da dora hotuna a shafukan zumunta, mutane na bukatar hoto ko bidyo mai inganci. hakan yana sa su kure saitin kyamarar su domin cimma burin su. Yin hakan yana haddasa zafin waya musamman ma idan aka dauki lokaci mai tsaho wajan daukar hotuna.
 6. Kure hasken fitilar gilashin waya (screen brightness). Idan hasken fuskar waya yayi yawa shima yana haddasa matsaloli kamar haka; Zafin waya, Zukewar Batir da kuma illata idanuwa.
 7. Amfani da Gurbatattun Manhajoji wadanda ke dauke da cutar na’urori (Virus). Mafi yawancin manhajoji da muke amfani da su musamman na kyauta (free apps) suna kunshe da tarin matsaloli kamar su; virus, bautar da waya wajan aiyuka marasa amfani, satar bayanan sirri, tallace-tallace masu ban haushi wadan da kan haddasa sankamewar waya a wasu lokuta da sauran su… wannan babbar matsalace da ke sanya dukkan manyan sassan waya su rage saurin aiwatar da aiki domin magance gobara saboda tsananin zafi. Karin bayani akan wannan a ziyarci wannan makala —>
 8. Yawan manhajoji masu kunna kansu (Startup Apps) a lokacin da manhajar sarrafa na’ura ke yunkurin bude waya (during booting…). Tabbas akwai wasu manhajojin da ake sakawa a waya wadanda sukan jefa kansu a cikin tsarin manhajoji masu kunna kansu lokacin waya ta ke yunkurin budewa, kuma sukan haddasa nauyin budewa, saboda sunkara mata aiki a lokacin. Shi ma yana haddasa karuwar zafi a waya.
 9. Manhajoji masu aiki a boye (background running apps). Akwai manhajoji da ke aiki a boye wasu suna da amfani, wasu kuma masu illa ne. Suma suna taka babbar rawa wajan kara zafin waya.
 10. Sarrafa waya a lokacin da at ke caji. Shi ma wannan yanada hadari, sarrafa waya a lokacin da take tsaka da caji yana haddasa tsananin zafi wanda ka’iya jawo konewar waya kurmus!
 11. Lulllube waya ruf ta yadda iska bazata ratsa ta ba. Amfani da jakar waya wadda ke rufe waya ruf, ta yadda iska bazata ratsata ba domin ta dan rage zafi. Hakan yana kara zafin waya.

Da sauran su…

Hanyoyin Magnace wannan matsala

Mafi yawancin dalilai ko matsalolin da na bayyana a sama ana iya magance su ta hanayar kashe waya ta huta na wasu mituna, sannan a sake kunnata. Musamman a wajan da babu karfin sadarwa.

 • A cire mata riga ko jaka wadda akan saka waya a ciki, domin ta samu iska a koda yaushe.
 • Sanya waya a kan tsarin hawa jirgin sama (Flight Mode) na dan wani lokaci domin katse dukkan wata sadarwa tattare da wayar.
 • Kawar da waya daga dukan hasken rana kai tsaye
 • A jiye waya a wajan da zata samu iska (Fan) amma kada a saka ta a cikin na’urar Fridge ko Freezer.
 • Rage hasken screen.
 • Cire manhajojin da basu da amfani.
 • Kashe manhajoji masu kunna kansu.
 • Kashe Bluetooth, Wifi da GPS a lokacin da ba’a bukatar su
 • Amfani da tsarin rage zukewar batir (Battery saver mode).
 • Kauracewa amfani da wasu manhajoji kamar su; Task Killer, RAM Booster da sauran su… Saboda suna wahalar da wayoyi ne su haddasa zafi da zukewar batir kawai.
 • Amfani da anti virus mai sauki kamar Avast ko Bullguard Bitdefender domin magance cutar na’urori ta virus.

Da fatan zamu amfana da wannan bayani.

Continue Reading