Connect with us

Wayoyin Zamani

Amfanin Rooting da Illolinsa ga wayoyin Android da iPhone

Published

on

rooting-da jailbrea

.

Amfanin Rooting da Illolinsa ga wayoyin Android da iPhone

Ba kamar Kwamfuta ba, wadda bata da iyaka dangane da irin aiyukan da ake gudanarwa da ita a kowanne bigire. Wayoyin Hannu ‘Yan zamani da suke gudanarda aiki akan tsari irin na kwamfuta, suna da iyaka ko takunkumi a dukkanin irin aiyukan da akeyi da su.

Mafi yawancin takunkumin da aka sakawa wadannan wayoyi na da matukar amfani wajan killacewa da bada kariya dangane da aiyukan da ake gudanarwa da su, ba tare da sanin masu amfani da su ba. To amma ta wata fuskar kamar an dabai-baye su ne, domin a duk lokacin da akayi nasarar cire takunkumi ga waya, za a samu damar yin abubuwa da yawa da kuma daga darajar sassan wayar domin cimma wasu manufofi masu yawa ta fuskar sarrafa wayoyin ‘yan zamani.

Saboda haka nake fatan fahimtar da masu amfani da samfuran wayoyin Android da iPhone a cikin wannan makaala.

Rooting: Yana faruwa ne akan waya samfurin Android. Domin cimma burin sani ko shiga wasu boyayyun sassa na tsarin sarrafawa, da kuma fito da wasu boyayyun hikimomi ko fasaha wadda zata bada damar sauya fasalin yadda wayar ke aiki sabanin yadda aka kera ta daga kamfani.

Idan har akayi nasarar rooting ga waya samfurin Android, za a cimma burin abubuwa da yawa, ga kadan daga cikin su;

  • Samun damar amfani da wasu manhajoji na musamman; akwai tarin manhajoji na musamman wadanda baza a sami damar aiki da su akan wayar android ba idan ba’ayi rooting ba. Saboda suna bukatar kololuwar izinin sarrafawa daga sassan wayar da suke akillace tun daga kamfani.
  • Damar sauya fasalin aikinta; kamar kara saurin masarrafi (CPU), wanda hakan yana nufin karawa ita kanta wayar hanzari wajan sarrafa aiki. Kara girman rumbun aiki (RAM) da kuma bude wasu rufaffun kofofi ko rufe budaddun kofofi, sabanin yadda aka kera ta a kamfani.
  • Zarce ka’idar aikin Na’ura; kamar sauya ka’idar manhajar sarrafawa, wadanda kamfanine ke da ikon yin hakan. Hakan yana sa wayar yin aiki na bam mamaki. Kamar sanya karamar waya tayi aiki kamar babbar waya.
  • Magance matsalar zukewar batir; wayar android ta kan zuki batir sosai dangane da irin manhajojin dake kanta da kuma yadda ake sarrafata. A lokuta da dama akan sami wasu boyayyun manhajoji da ke aiki a boye, hakan yakansa zukewar batir da wuri. Ta hanyar rooting ne kadai za a iya dakile aiyukan su domin bunkasa lokacin batir.
  • Dakile kutsen tallace-tallace masu ban haushi; ana shan fama da kutsen tallace-tallace ko hotuna a lokacin da ake aiki da wayar android, wasu lokutan ma sukan hana gudanar da aikin da akeyi a lokacin. Amma idan akayi rooting ana samun damar toshe kofofin da suke samun damar kutsawa.
  • Zamowa oga wajan sarrafa wayar ka; idan har kayi nasarar rooting ga wayar android, ka zamo oga wajan juya akalar wayar ka, za ka iya yin duk aiyukan da ka keso da ita kamar kai ka kera ta. Masu kutse suna amfani da wannan fasaha ta rooting domin samun damar aiwatar da miyagun aiyukan su a ko ina.

Dukkanin wadannan abubuwa da na dan tsakuro nayi bayani akai, daidai suke da abubuwan da ke faruwa ga wayoyi samfurin iPhone da akewa lakabi da Jailbreak.

Illolin rooting ko Jailbreak

Duk wayar da akayi nasarar cire takunkumi (rooting ko jailbreak) a gareta, to kuwa ta fada cikin hadari ta fuskoki da dama. Ga kadan daga cikin su;

Samun damar sauya tsarin yadda take aiki; hakan yana nufin za’a iya sauya fasali ko tsarin yadda take aiki wanda hakan ka iya jawo rashin karkon wayar, ko konewar wasu sassan ta. Komai zai iya faruwa kamar gogewa ko gurbatar wasu daga cikin jigajigan manhajoji da sauran su..

Rushewar yarjejeniyar kamfani (Waranty); da zarar anyi rooting, duk wata yarjejeniya da kamfani ya tsara tsakaninsa da abokan hulda wajan bada kulawa kyauta a duk lokacin da aka sami tangarda da na’ura kafin karewar wa’adi mafi akasari shekara daya, duk ta warware. Asara ta hau kan ka, babu ruwan kamfani. Wannaa dalili ya sanya duk manhajojin da ake amfani dasu wajan rooting ko jailbreak, sukan yi gargadin cewa “duk abinda ya biyo baya, babu ruwan su. Dan haka kayi kana sani”

Matsala wajan sabunta manhaja; idan akayi rooting akan rasa damar sabunta manhajar sarrafawa da sauran manhajoji masu muhimmanci akan waya. Kuma idan akabi wasu hanyoyi domin sabuntawa akan sami matsala saboda sauya tsarin wayar da akayi ba bisa ka’ida ba. Wayar zata iya lalacewa gaba daya (Crashing).

Bude kofofin cututtuka ga waya; manhajojin da ake amfani da su wajan yin rooting, mafi yawancin su gurbatattune, cinkushe suke da sirkullen masu kutse. Dazarar an saka su (install) zasu bude kofofin nadar bayanan sirri da sauran abubuwa marasa dadi, idan har ba ayi amfani da maganin cutar na’ura (anti-virus) mai karfin gaske ba.

Da wadannan bayanai nake jan hankali akan cewa, a lokuta da dama mu muke bada kai bori yake hawa, mu muke saka gurbatattun manhajojin da suke haifar da matsalolin da muke ta fama da su a yanzu. Kamar yadda ake ta fama da matsalolin kutse a shafukan zumunta da sauran su…

Idan kunne yaji, jiki ya tsira
Kuma idan da kwadayi…..

Continue Reading