Connect with us

Manhaja

Amfani da manhajar Windows 7 na cikin garari

Published

on

manhajar windows 7

A karshen shekarar 2019 ne amfanin samara da manhajojin sarrafa na’urar Kwamfuta wato Microsoft ya sanar da Duniya cewa daga 14 ga watan Janairun 2020 zai dakatar da sabunta matakan tsaro na manahajara Windows 7.

Dukkanin kulawar da ita wannan manhaja (ta windows 7) take samu a lokuta da dama ta fuskar ingantawa da kuma kara karfin matakan tsaro domin kare masu amfani da ita daga dukkanin barazana daga cututtukan na’ura (virus da dange-dangen su), ingata sadarwa tsakanin na’urori da intanet har zuwa kariya tsakanin masu kutse domin satar bayanai a cikin na’urori.

Kamfanin Mocrosoft ya kara da cewa bayan 14 ga watan Janairun shekara ta 2020, za a iya cigaba da mafani da manhajar windows 7 amma fa babu tsaro ga dukkan barzanar cuta ko kutse a tattare da wannan manhaja ta windows 7. Dan haka duk wanda yake da sha’awar cigaba da amfani da wannan manhaja ta windows 7, zai yi ne yana sani domin babu kulawa (support) daga kamfanin.

Hakan babbar barazana musammam ga manyan kamfanoni a duniya masu ta’ammali da manhajar sarrafa na’ura na Microsoft Windows 7. Kamfanonin hadahadar kasuwanci da kudade ta kafar yanar gizo na iya fuskantar barazanar kutse da satar bayanan sirri da sauran su.

Shawara anan itace kowa ya koma amfani da Windows 8, 8.1 ko Windows 10 wadanda sune a halin yanzu ake basu dukkan kulawar da ta dace, ta fuskoki da dama. Kama daga ingantawa (Update) har zuwa kara karfin matakan tsaro (security updates) da kuma karbar korafi dangane da targardar da za’a ci karo da ita yayin sarrafawa (Support). Da sauran su…

Continue Reading