Connect with us

Manhaja

Amfani ko Rashin Amfanin manhajar GBWhatsApp

Published

on

manhajar whatsapp

Amfani ko Rashin Amfanin manhajar GBWhatsApp

Wannan al’amari ne da kullum nake samun tambaya akan sa, duba da yadda whatsapp ya zamo jigo a rayuwar Jama’a wajan sada zumunta, mu’amalar Kasuwanci da sauran al’amura masu yawan gaske. Wannan dalili ya kawo sauye-sauye a cikin manhajar WhatsApp na asali domin dabbaka wasu sassa daga cikin sa domin samun damar yin abubuwan da WhatsApp na asali bazai bari ayi ba.

GBWhatsApp da dange-dangensu an samar dasu ne ta hanyar bude manhajar asali ta WhatsApp domin sauya tsarin manhajar ta fuskoki kamar ka’idodin yadda manhajar take mu’amala da duk na’urorin da aka dora manhajar akai, wanda hakan yaci karo da sharuddan kamfanin manhajar ta asali.

Ire-iren wadannan manhajoji da aka jirkita tsarin su na asali, domin cimma wata manufa kamar yadda na bayyana asama. Amfani da su yanada hadari ko illa ga bayannan sirri ko kuma haddasa kamuwar cututtuka ga na’urar ko wayar da ake amfani da wannan manhaja akai. Saboda babu cikakken tsaro, sannan kuma sakonnin da ake musaya da wannan manhaja basu da hurumi akan babbar na’uarar kamfanin whatsappa na asali. Ga kadan daga cikin matsalolin dake faruwa.

Matsala ta farko; Suna da saurin kamuwa da cututtukan na’uraawto Virus da dange-dangen su, saboda rashin kariya ko tsaro. Hakan yana bada damar satar bayannan sirri da kuma salwantar bayanan gaba daya.

Matsala biyu; Yin duk wata mu’amala da ta shafi banki ko harkokin kasuwanci na da hadari kasancewar komai ya dude yadda wasu za su iya datsar bayanai a hanya. Dukkanin matakan tsaro na hanyoyin sadarwa na asali sun rushe gaba daya.

Matsala ta uku; Amfani da GBWhatsApp ko WhatsApp Plus da sauran su, babu laifi a shar’ance. Amma dai sun karya duk wata ka’ida ta amnhajar WhatsAppa na asali. Sannan kuma akwai yiwuwar kamfanin WhatsAppa ya toshe ko rufe layukan da ake amfani da su akan wadancan manhajojin.

Matsala ta hudu; wadannan manhajoji sukan addabi masu amfani da su wajan neman izini (permission) domin sarrafa wasu sassa musamman na sirri. Hakan babbar matsalace idan ya kasance ana amfani da wayar ko na’urar wajan harkokin kasuwanci da sauransu… Suna da abubuwa da tsari da kowa zai so yayi amfani da su a maimakon WhatsApp na asali, amma cinkushe suke da illoli ga masu amfani da su.

Matsala ta biyar; duk wanda yake da bukatar yin amfani da wadannan manhajoji da aka jirkita tsarin su na asali, yanada kyau ya sani cewa duk abinda ya faru dashi ko wayar sa, babu alhakin wadanda suka samar da su. Amsu iya magana sunce maganin ba dadi, kada afara. Da muguwar rawa gara kin tashi.

Kadan daga cikin amfanin sa

Na farko; wannan gurbatacciyar manhaja tana bada damar yin sauye-sauye ta fuskar kara girman abubuwan da ake musaya fiye da yadda aka tsarawa manhajar asali, ana iya tsara fuskar manhajar yadda ake da bukata, ana iya kara girman haruffa da sauya fasalin rubutu har ma a sanya musu launika yadda ake so, da sauran al’amura masu yawa na burgewa da kayatarwa.

Na biyu; wannan manhaja tana bada damar sarrafa lokacin mu’amala, da kuma damar sankamar da lokaci ta yadda babu wanda zai gane lokacin da ka hau ko ka sauka daga manhajar. Haka kuma yana bada damar boye status ga wasu daga cikin mutanen da ake mu’amala da su.

Kadan daga cikin rashin amfanin sa

Na daya; za a iya fuskantar dakatarwa ko toshewa daga matattarar bayanai ta sahihiyar manhajar whatsapp, ma’ana za’a dakatar ko toshe layukan da ake amfani da su a whatsapp har sai an koma amfani da ta asali. hakan ya taba faruwa a shekarar 2015 da kuma 2019 lokacin da yawan masu amfani da gurbatattun manhajar whatsapp suka yawaita a duniya.

Na biyu; rashin sabunta manhaja da kanta (automatically), sai dai a sauke sabuwar manhaja domin sabuntawa (manually). Dole ne mutum ya dinga bibiya akai-akai domin samun sabuwar manhajar, wadda ke kunshe da tsarin magance dakatarwa ko toshe layi kamar yadda na bayyana a sama.

Akwai nau’i-nau’i na wannan manhaja wadda kuma kowanne yana kunshe da irin nasa hikimomin da masu amfani da su ke kallo a matsayin cigaba. Kua ga masu bukata za su iya sauke su a wayoyin su ko na’urorin su.

 1. WhatsApp Plus
 2. GBWhatsApp
 3. YOWhatsApp
 4. FMWhatsApp
 5. OGWhatsApp
 6. WhatsApp Prime
 7. WhatsApp MA
 8. WhatsApp Indigo
 9. GBWhatsApp Mini
 10. Soula WhatsApp Lite
 11. YCWhatsApp
 12. ZE WhatsApp
 13. WhatsApp Tweaker
 14. BSEWhatsApp
 15. Delta GBWhatsApp
 16. WhatsApp Pro
 17. KRWhatsApp

Dukkanin wadannan nau’i-nau’i na manhajar whatsApp kowanne yana da irin hikimar da ke cikin sa, to amma dukkanin su sun karya ka’idojin manhajar ta asali. Sannan kuma akwai yiwuwar samun matsaloli masu yawa bayan wadanda na ambata a sama.

Continue Reading