Connect with us

Featured

An bukaci haramta amfani da motoci masu gurbata muhalli

Published

on

Hayakin ababen hawa guba ne

Wani sabon gangami da aka yi wa lakabi da ”Talla mara kyau” ya bukaci a hanzarta dakatar da tallan motoci masu gurbata muhalli.

Gangamin ya ce gwamnati ta dakile tallata motocin tsere samfurin SUV a matsayin hanyar rage fitar da hayakin da ke gurbata muhalli.

Kakakin kamfanin kera irin wadannan motoci ya ce a yanzu babu motar da ta kai SUV dadin hawa a tarihi, kuma ya ce da damansu na iya amfani da batura.

Sai dai daya daga cikin masu jagorantar fannin ilimi a Burtaniya ya ce ci gaba da sayar da irin wadannan motoci da ke fitar da hayaki na iya karya dokokin da kasar ta cimma na rage gurbata muhalli, don haka tilas a haramta su.

Wani kakakin gwamnati ya ce: ”Mu na kokari wajen samar da tsarin sufuri marar gurbata muhalli domin cimma muradan mu kafin shekara ta 2025.

”Sannan muna wayar da tallata manufofin mu ga mutane saboda mu taimaka musu wajen yin zabi a sayer motar hawa.”

Motocin samfurin SUV, sune kashi 4 cikin 10 na sabbin motoci da ake cinikinsu a Burtaniya, sannan motoci da ke amfani da wutar lantarki kuma basa wuce biyu a cikin dari.

Rahoton green think tank, wata sabuwar cibiyar bincike kan yanayi da muhalli na cewa yayin manyan motocin na faruwa ne sakamakon yadda masu talla ke jan hankali da kwadaita mutane.

Fargabar karuwar irin wadannan motoci na kasaita da cinikinsu musamman SUVs da ke gurbata muhalli babbar barazana ce wajen cimma muradai a kan yanayi.

Motoci

Wanda ya wallafa wannan rahoto ya ankarar da cewa ko motocin da ke amfani da wutan lantarki ba zasu shawo kan duk matsalolin da ke tattare da SUVs ba.

Ya ce ya shaida hakan ne saboda motocin za su ci gaba da gurbata muhalli ta hanyar sinadaran da suke fitarwa daga burkin mota da tayoyi, da kuma amfani da sinadarai masu sanya batur ya yi nauyi.

Zabin da aka fi yi

A yankunan birane, motocin SUVs sun yi yawa, a cewarsa.

Rahoton ya gano motoci 150,000 sabbi a kan titin sun yi yawa a Burtaniya inda ake fama da wurin ajiye mota.

Wannan na zuwa ne yayin da mahukunta a kasashe ke kokarin fitar da hanya a tituna da masu tafiya da kafa da keke za su ke bi.

Ma wallafin na son a haramta tallata motocin da ke fitar da hayakin da ya kai 160g a tafiyar kilomita 2, da wadanda ke zarta tsayin mita 4.8.

Andrew Simms, daya daga cikin mawallafan, ya ce: ”Mun kawo karshen tallar taba bayan mun gano barazanar da shan taba sigari ke da shi ga lafiyar al’umma.

”Yanzu da muka fahimci lafiyar jikin dan adam da kuma illar da hayakin mota ke da shi ga muhalli, lokaci ya yi da ya kamata mu daina tallar da ke sake tsananta yanayin da ake ciki.

”Akwai talla, sannan akwai talla mara kyau, wanda ke karfafa fitar da gurbatacciyar iska mafi muni da motocin SUV ke yi, don haka akwai bukatar dakatar da hakan.”

Cunkoson ababan hawa

Amma Mike Hawes, na kungiyar masu masana’antar kerawa da cinikin motoci, ya shaida wa BBC cewa: ”SUV na sake bijiro da sabbin zabi.

”Idan za a bada misali da motar kirar SUV da ake yi yanzu kusan ba sa fitar da yawan hayakin kuma wanda suke fitarwa baya gurbata muhalli, sannan sabbin motocin na zuwa da zabin amfani da lantarki.

”A yau wadannan motoci sun kasance irinsu mafi tsafta a tarihi, inda gurbatacciyar iskar da suke fitarwa ta yi kasa da kashi 43 cikin 100 adadin mafi kankanta tun bayan shekara 20.”

‘Babu Bambanci’

Kungiyoyi kananan hukumomi da ke wakiltar yankunansu, na fargabar yayin manyan motoci.

Kakakinsu ya shaida wa BBC: ”Bukatar wuraren ajiye mota zai koma karamin wuri. Masu motoci zai kasance suna biyan kudi mai yawa na ajiye mota da jiran dogon lokaci kafin su samu wuri.”

Shin haramcin talla zai yi aiki? Steve Gooding, na gidauniyar RAC ya ce: ”Mutanen da ke kashe £70,000 kan sabuwar mota ba wai talla ke ingiza su ba – kawai suna kwadaituwa ne da matsayin abin da suke sha’awa. Bana jin daina talla zai haifar da wani gagarumin sauyi.”

Bugu da kari, an wallafa wannan rahoton a dai-dai lokacin da masana’antun motoci a Burtaniya, ke cikin matsi sakamakon tasirin annobar korona.

Amma Farfessa Jillian Anable, na jami’ar Leeds na cewa gwamnati na bukatar fahimtar abubuwan da ake nufi a kan motocin – da duba yi wuwar haramta kera manyan motocin da ke gurbata muhalli.

”Akwai bukatar mu soma tunani kan yadda za’a hana sayar da manyan motoci a kasuwannin Burtaniya.”

Ta kara da cewa: ”Binciken mu ya nuna yadda ake kokarin kawar da motoci masu gurbata muhalli a cikin shekaru 10 zuwa 15 masu zuwa, hakan zai fi dacewa watakil kafin nan duniya ta soma karkata daga amfani da man fetur ko diesel.”

Tushen Labarin

Continue Reading