Connect with us

Featured

An cire shafin Nnamdi Kanu a Facebook

Published

on

An cire shafin Nnamdi Kanu a facebook

 

Facebook ya cire shafin shugaban ƴan awaren nan na IPOB a Najeriya, Nnamdi Kanu, bayan wani bidiyo da ya fitar ranar Talata inda yake zargin makiyaya da lalata gonaki.

Wannan na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fama da rikici tsakanin manoma da makiyaya a sassa da dama na ƙasar.

Mista Kanu ya wallafa bidiyon wasu mutane da ake zargin ƴan kungiyar Eastern Security Network ne – wata kungiyar mayaƙan sa kai a kudu maso gabashin Najeriya – suna karkashe shanu a unguwannin makiyaya.

Mai magana da yawun Facebook ya shaida wa BBC cewa burin kamfanin shi ne “bai wa mutane damar yin magana” amma kuma yana so mutane su “san cewa suna cikin tsaro” a lokacin da suke kan shafin.

A wata sanarwa, Facebook ya ce cire shafin Nnamdi Kanu ya bi tsarin dokokinsa ne na wallafa sakonni masu dauke da kalaman ɓatanci.

Wani dan kungiyar na Eastern Security Network ya ce za su daukaka batun haramcin. Haka kuma, ya ce haramcin bai shafi Radio Biafra ba da sauran sauran shafukan ƙungiyar.

Shafin Nnamdi Kanu dai ya kasance dandalin ƴan IPOB a faɗin duniya.

Gwamnatin Najeriya ta haramta kungiyar sannan ta ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci a 2017.

Wane ne Nnamdi Kanu?

Mista Kanu, wanda ke da izinin zama dan kasa na Najeriya da Birtaniya, ya ƙirƙiri kungiyar People Of Biafra (Ipob), a shakarar 2014 domin neman kafa kasar Biafra.

“Idan akwai wani bangare na Najeriya da ke son shiga yankin na Biafra, to muna musu maraba, matukar sun yi amanna da karantarwar addinan Yahudu da Kiristanci…tsarin karantarwar da kasar Biafra ta ginu a kansa.

Shirin samar da kasar Biafra dai ba sabon abu ba ne.

A shekarar 1967 shugabannin kabilar Igbo sun ayyana kasar Biafra, bayan wani mummunan yakin basasa, wanda ya jawo mutuwar kusan mutum miliyan daya, amma an samu galaba a kan masu neman ballewar.

Mista Kanu shi ne na baya-bayan nan a kabilar Igbo da ke fafutukar ci gaba da gwagwarmayar neman kafa kasar Biafra.

Taswirar Najeriya

 

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku