31 C
Kano
Thursday, October 22, 2020

An fara kauracewa shafukan Facebook da Instagram

Mafi Shahara

Kim Kardashian West da wasu gwamman fitattun mutanen sun sanar da cewa za su rufe shafukansu na sada zumunta don nuna adawa da ”yaɗa ƙiyayya da farfaganda da ba da bayanai ba daidai ba.”

Television personality Kim Kardashian West
Television Personality Kim Kardashian West – Reuters

A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, Kardashian West ta ce: ”Bayanan da ake yaɗawa ba daidai ba a shafukan sada zumunta na da illa matuƙa.”

Matakin nata wani ɓangare ne na fafutukar #StopHateforProfit wacce masu fafutukar ƴancin fararen hula suka shirya.

Fitattun mutanen za su rufe shafukan sada zumuntarsu na tsawon sa’a 24 a ranar Laraba.

Kardashian West ta ce: ”Ba zan iya zama na yi shiru a yayin da waɗannan shafuka suek ci gaba da yaɗa ƙiyayya da farfaganda ba adabayanai ba daidai ba – waɗanda wasu ƙungiyoyi ke ƙirƙiri don raba kan Amurka.”

Ta ƙara da cewa: ”Bayanan da ake yaɗawa waɗanda ba daidai ba a shafukan sada zumunta na da mummunar illa kan zaɓukanmu tare da durƙusar da dimokraɗiyyarmu.”

Sauran fitattun mutanen sun amince da bin sahun ƙauracewar wa danda suka haɗa da jarumi Leonardo DiCaprio da Sacha Baron Cohen da Jennifer Lawrence da kuma mawaƙiya Katy Perry.

“Ba zan zauna na zura ido ina kallon yadda waɗannan shafukan suke yi kmaar ba su san da waɗannan ƙungiyoyi ba ta hanyar yaɗa bayanan da ba daidai ba,” kamar yadda Perry ta rubuta a Instagram.

Tauraron fina-finai Ashton Kutcher, wanda ke da miliyoyin mabiya ya kuma bi sahun ƙauracewar, ya ce ”ba a gina waɗannan shafukan don yaɗa ƙiyayya da rikici ba”.

Katy Perry and Orlando Bloom
Katy Perry da Orlando Bloom ma sun bi sahun auracewar – Getty Image

Waɗanda suka shriya gangamin #StopHateforProfit campaign, wanda aka ƙaddamar da shi a Yuni, sun soku Facebook da Instagram cewa ba sa taɓuka abin kirki wajen hana yaɗa kalaman ƙiyayya da bayanai ba daidai ba.

Ƙungiyar ta fi mayar da hankali kan kamfanin Facebook, wanda shi ne mamallakin Instagram da kuma WhatsApp, kuma a bara ya samu kuɗin ta hanyar talla har kusan dala biliyan 70.

Dubban kamfanonin kasuwanci da manyan ƙungiyoyin fararen hula sun sanya hannu kan fafutukar.

A watan Yuni Facebook ya ce zai ɗauki matakai kan duk wasu saƙwanni na cutarwa a shafinsa.

Haka kuma mamallakin kamfanin Mark Zuckerberg ya ce zai haramta wallafa tallace-tallacen da ke ɗauke da barazana ga ”wasu mutanen naƙabilu ko launin fata ko addinai ko aƙida ko jinsi daban-daban.

A wata sanarwa da ya fitar ya ce: ”Tuni an shiga matakin zafin siyasa saboda ƙaratowar zaɓuka, Facebook za ta ɗauki ƙarin matakai don tabbatar da cewa kowa ya kasance cikin aminci.

Amma fafutukar #StopHateforProfit na kira ga a ƙara ɗaukar matakai, kuma fiye da kamfanoni 90 sun dakatar da bai wa Facebook tallata don goyon bayan wancan ƙoƙarin.

Tushen Labarin

Karin Wasu

Sababbin Wallafa