Connect with us

Featured

An fito da matakin daƙile kalaman zagi a dandalin Twitter

Published

on

dandalin twitter

Daga yanzu shafin Twitter zai ƙara matsin lamba ga masu amfani da “kalaman zagi ko kalmomin da basu dace ba” kafin su wallafa su a dandalin na Twitter.

Dandalin sadarwar na Twitter ya sha fuskantar suka akan kalaman rashin kyautawa, kuma ya fara gwajin tsarin tantance kalaman batancin tun a shekarar da ta gabata.

Twitter ya ce sakamakon gwajin ya nuna raguwar yawan amfani da kalaman zagi a dandalin.

A ranar Laraba ne kamfanin ya ce zai bai wa masu amfani da turanci damar fara amfani da tsarin a kan wayoyin iPhone da Android.

Shafin na Twitter ya ce matsin lambar ta sanya kaso 34 cikin 100 na masu amfani da Twitter sauya saƙon da suka yi niyyar wallafawa ko kuma fasa turawa gaba ɗaya.

A cewarsa, masu amfani da shafin sun rage wallafa zage-zage ko cin zarafi da kaso 11 cikin 100 bayan an matsa musu a karon farko.

Haka zalika, suma ba lallai ne a zage su ba ko kuma yi musu kalaman ɓatanci.

Bugu da ƙari dandalin Twitter yana amfani da makamancin wannan tsari domin rage yaɗa labaran ƙarya, inda ake matsa wa mutane shigar da adireshin wani labari da suke son yaɗawa su karanta kafin su sake yaɗa shi.

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku