Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu ƴan Kano da ke cin zarafin mata ta hanyar lalata tare da yaɗawa a WhatsApp.

Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan Frank Mba ya aikawa BBC ta ce jami’an ƴan sandan ƙasa da ƙasa ta Interpol a Abuja ne suka kama mutanen da ke sayar da bidiyo da hotunan batsa a shafin WhatsApp mallakin wani ɗan ƙasar Brazil.

Daga cikin kayayyakin da aka samu hannun mutanen da ake zargi sun haɗa da wayoyin salula uku da kamfuta ta Laptop. Kuma ƴan sandan sun ce sun samu bidiyo da dama na ƴan mata ƴan ƙasa da shekara 18 da aka sayar a Intanet.

Rundunar ƴan sandan ta ce ta kama su ne ta hanyar bayanan sirri da ta samu daga jami’an Interpol a Brasilia.

Rundunar ƴan sandan ta kuma ce ta kama waɗanda take zargi masu yin garkuwa da mata da ƙananan yara a jihohin kudu masu kudancin ƙasar.

Kuma tana tsare da mutum biyar da ke garkuwa da mata da ƙananan yawa a yankunan jihar Fatakwal.

A cikin sanarwar, sufeton ƴan sandan Najeriya ya ce shirin rundunar da aka aiwatar don magance cin zarafin mata da ƙananan yara a Najeriya ya fara samar da kyakkyawan sakamako.

Sanarwar ta bayyana sunayen waɗanda ta take zargi masu satar matan da ƙananan yara kuma dukkaninsu ƴan asalin jihohin kudu maso kudu ne.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana lokacin da aka kama su ba da kuma inda aka kama su.

Sanarwar ta kuma ce jimillar mutum 2,792 ta kama da take zargi da aikata laifuka da suka shafi cin zarafin mata a shekarar 2020. Ta kuma ce tana ci gaba da gudanar da bincike kafin gabatar da su kotu.

Sufeton ƴan sandan Najeriya ya yi kira ga iyaye su sa ido sosai kan ƴaƴansu tare bayar da rahoto kan duk wani nau’in cin zarafi da aka yi wa mata da yara ƙanana.

Tushen Labari