Connect with us

Fasaha

An kirkiro manhaja mai magana da Hausa

Published

on

Manhaja-Mai-Magana-Da-Hausa

Wasu matasa ‘yan asalin arewacin Najeriya sun kirkiri wata fasaha mai tunani irin na dan adam da suka yi wa lakabi da suna Amina.

Fasahar wadda ta ci sunan sarauniya Amina ta Zazzau na amsa tambayoyi ne a harshen Ingilishi da na Hausa dangane da bayanai da suka shafi annobar korona.

Amina dai ba batun-butumi ba ce wato mai zati irin na dan adam, fasaha ce mai kwakwalwar dan adam da ake tattaunawa da ita a kan intanet da ake kira ‘chatbot’.

Za a iya cewa Amina ce fasahar bot irinta ta farko da aka kirkira da harshen Hausa.

Al-amin Bugaje wanda daya ne daga cikin wadanda suka kirkiri wannan fasaha, kuma dalibi a jami’ar Imperial College da ke Landan ya shaida wa BBC cewa “abu na gaba da muke son yi shi ne samar da damar aikewa da sakon murya ga Amina maimakon rubutu.”

Ya kara da cewa “mun kirkiri Amina ne domin bai wa masu magana da harshen Hausa gudunmowa dangane da bayanan da suka shafi annobar korona.”

To sai dai da aka tambayi Bugaje kan ko akwai yiwuwar samar da butum-butumi na Amina sai ya ce “abin da kamar wuya a samu hakan a nan kusa sai dai nan da wasu ‘yan shekaru.”

TUSHEN LABARI