Connect with us

Manhaja

An kirkiro manhajar da zata hana yada hotunan tsaraici a kafafen sada zumunta

Published

on

manhajar tace hotunan tsiraici

A halin yanzu an kirkiro wata manhaja mai suna SAFE DM wadda aikinta shine bincika sakonni musamman wadanda suke dauke da hotuna, domin gano hotunan tsaraici sannan kuma ta goge su. Bayan ta goge su zata aika da sakon cewa “WANNAN HOTO KO HOTUNA BA SU DACE BA”.

Kelsey Bressler, itace wadda ta kirkiro wannan manhaja a ranar Juma’ar shekaran jiya 14 ga watan Fabrairu, bayan tasha fama da ire-iren sakonnin tsaraici da ake yawan aika mata dasu.

Hakika kamfani ko shafukan zumunta suna da cikakkiyar dama akan hanyoyin da zasu yi amafni da su wajan dakile  dukkanin sakonnin da basu dace ba, masu gurbata tarbiyya. Kelsey Bressler ita da abokan aikinta sun tabbatar da cewa manhajar tayi aiki kaso casa’in da tara cikin dari (99%).

Wannan manhaja ta SAFE DM an fara jarrabata ne a shafin TWITTER. Kelsey Bressler, a lokacin da zata jarraba aikin wannan manhaja, ta sanar a shafinta na twitter cewatana so ta jarraba wata sabuwar manhaja da take kan aikin kirkirarta wadda zata zate hotunan tsiraici daga cikin sakonni da ake aikawa ko yadawa. Saboda tayi umar ni da a aika mata da sakonnin hotunan tsiraici. Anan take aka aiko mata da hotuna sama da dubu hudu (4000), kuma duk wannan sabuwar manhaja ta kama su ta goge hotunan tsiraicin dake cikin sakonnin duka. Kamar yadda ta bayyana a shafinta na twitter.

Safe dm - duniyar fasaha

Sakamakon da ya biyo bayan gwaji da tayi na wannan manhaja ya tabbatar da cewa manhajar tayi aiki kamar yadda aka tsarata. Kuma ga duk wanda yake son wannan mahaja ta SAFE DM zai iya  sawa a shafin sa na twitter domin ganin aiki da cikawa.

Daga wannan gwaji da aka yi nasara, akwai yiwuwar cigaba da fadada wannan manhja harzuwa kan sauran shafukan zumunta domin dakile hotunan tsaraici/batsa. kamar yadda Kelsey Bressler ta dora akan jawabinta.

Duniyar Fasaha Online