Connect with us

Fasaha

An Sace Manhajar eNaira.

Published

on

enaira
Sabuwar Manhajar eNaira da aka kaddamar ta bace daga Google Playstore

Sabuwar Manhajar eNaira da aka kaddamar ta bace daga Google Playstore kwatsam, kuma tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi tsokaci da cewa watakila anyi garkuwa da ita manhajar ta eNaira.

Duniyar Fasaha Online ta lura a ranar Alhamis cewa manhajar eNaira na kan Play Store da misalin karfe 12:07 na dare (Agogon Najeriya) daga nan kuma ba’a sake ganin ta a rumbun manhajojin Google Play Store ba.

Har yanzu ba a san dalilin bacewar manhajar ba.

Shehu Sani a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis ya ce “watakila an sace manhajar eNaira daga shagon Google.”

Wani dan Najeriya mai amfani da Twitter Dr Penking ya ce, “Google Play Store ya goge manhajar eNaira saboda korafe-korafe da aka samu akan manhajar.”

Babban bankin Najeriya a ranar Laraba ya gargadi jama’a game da wani sakon Twitter (@enaira_cbdc) da ke nuna cewa Bankin yana fitar da eNaira kimanin biliyan 50.

Bankin ya ce wasu ‘yan damfara suna ta yada sakonnin da suka shafi kudaden da suke zaburar da ‘yan Najeriya cikin aikata muggan laifuka da ta’addanci.

Ta ce hakan bashi da alaƙa da kazafin wannan kafa ta Twitter da bata aiki tun lokacin da gwamnati ta dakatar da dandalin microblogging a Najeriya.

Muna bukatar ra’ayoyin ku akan wannan batu a bangaren tsokaci (Comment Section)

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku