Connect with us

Shafukan Zumunta

An sami daukewar sabis ga Shafukan Instagram da Whatsapp kusan sa’a daya

Published

on

shafukan zumunta

An sami daukewar sabis ga Shafukan Instagram da Whatsapp kusan sa’a daya.

an sami katsewar service ga shafukan instagram da whatsapp sun tsaya cak kusan sa’a daya.

An sami katsewar service ga shafukan instagram da whatsapp sun tsaya cak kusan sa’a daya.

Aikace-aikacen shafukan sada zumunta na Facebook da WhatsApp da Instagram sun gamu da matsala a yammacin jiya Juma’a. Yawancin masu amfani da shafin sun yi korafi kan rashin iya aikawa ko karban sakonni a Whatsapp, yayin da da yawa suka ce sun kasa dora hotuna da bidiyo a shafin Instagram.

Wasu kuma sun kokawa sukayi  game da samun matsala wajan amfani da Facebook, amma da yawa sun ce manhajar su na aiki daidai.

Masu amfani da shafukan sun fara ba da rahoton matsalar da misalin 04:25 na yamma.  Aiyukan shafukan ya dawo daidai da misalin 05:12 na yamma.

Har yanzu ba a san abin da ya haifar da matsalar ba saboda babu wata sanarwa a hukumance daga cibiyar kamfanin na Facebook. Yawancin masu amfani da shafukan a faɗin duniya, kamar Indiya, sun shiga Twitter don yin rahoto game da faruwar al’amarin.

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku