Connect with us

Fasaha

Babu alaaka tsakanin fasahar 5G da coronavirus

Published

on

fasahar 5g da corona virus

Babu alaaka tsakanin fasahar 5G da coronavirus

Wannan al’amari ya haifar da rudani a tsakanin al’umma musamman mazauna kasar birtaniya wato Ingila (England), a lokacin da aka yada wannan labari ta kafafen sada zumunta.

A karshen shekarar 2019 aka sanar da duniya irin rormon da ke cikin fasahar 5G, wato tsananin sauri da fasahar ke dashi wajan isar da sako ko sauke abubuwa daga shafukan intanet, fiye da su fasahar 3G da 4G. Kuma har aka shelanta cewa za’a fara amfani da ita a wasu manyan kasashe na duniya a cikin shekarar 2020.

Wannan al’amari ya faru ne  abisa wata hira da aka wallafa a 22 ga watan Janairun wannan shekara. Hirar anyi tane da wani masani a fannin lafiya inda ya furta cewa “Fasahar 5G tana da illa ga rayuwar bil’adama, amma ba kowa ne ya fuskanci hakan ba” kuma ya gaza bayyana dalilan da za su tabbatar da hakan. Duk da cewa kamfanin jaridar yayi kokarin cire wannan hira daga shafin intanet din su, tuni labarin ya watsu ta kafafen zumunta. wanda ahakan ne ya tun zura jama’a har suka fara kona turakun 5G dake can kasar ingila.

A cikin hirar da akayi da shi wancan masani a fannin lafiya. Ya alakanta cewa Wuhan dake kasar China canne sashen da aka fara jarraba aiki da fasahar 5G, wanda a fadar sa hakan ne ya jawo wannan annoba ta coronavirus. Har ya kara da cewa fasahar 5G tana zuke iskar da ‘yan adam suke shaka (Oxygen). Amma fa duk wadannan batutuwa da yake ya gaza bada hujja ko shaida wajan tabbatar da hakan. Kamfanin jaridar yayi nadamar wallafa wannan hira mara hujjoji. Akwai kasashe da wannan annoba ta mamaya wadanda ko kamshin 5G ba suji ba domin ba’a saka su a lissafin kasashen da zasu fara amfani da fasahar ba kamar su Japan, Iran da sauran su…

Har yanzu babu wasu hujjoji na kimiyya da suka nuna cewa fasahar 5G da coronavirus suna da alaaka. Fasahar 5G tana amfani da babban matakin zangon tururin sadarwa (higher frequency of radio waves) fiye da fasahar 4G da 3G. Nan take hukumar da ke kula fasahar sadarwa ta kasar birtaniya suka dukufa wajan sake gwaje-gwaje akan karfin tururin fasahar 5G, wanda sakamako ya bayyana gaskiyar al’amarin sabanin yadda aka yada jita-jita. Wannan ya tabbatar da cewa babu alaaka tsakanin su.

Wannan faifan bidiyo yana nuna yadda kwararru ke aikin gwajin karfin tururin fasahar 5G. Shi yasa yada labarin kanzon kurege ko jitajita bashi da amfani.