Connect with us

Fasaha

Bambanci tsakanin shafukan intanet masu HTTP da masu HTTPS

Published

on

bambanci-tsakanin-http-da-https

Bambanci tsakanin shafukan intanet masu HTTP da masu HTTPS

Lallai akwai bukatar kara samun fahimta akan wadannan al’amura guda biyu, duba da yadda amfani da shafukan intanet ya zamo babban ala’amari a dukkan bukatun mu da aiyukan mu na yau da kullum. kuma a lokacin da ake da bukatar tsaro a lokacin gudanar da harkokin kasuwanci ko musayar bayanan sirri ta kafar intanet.

Da farko me ake nufi da HTTP?

AMSA: Cikakkiyar Jumlar wadannan haruffa http; Hypertext Transfer Protocol. A duk lokacin da ake da bukatar shiga ko bincike ko watayawa a shafukan intanet, akwai bukatar a rubuta adreshi a inda ake saka adreshi daga sama a manhajar hawa intanet (browser). Kamar haka http:// , kuma yana amfani da tsari ko ka’idodin fasahar TCP wajan aikawa da karbo sakonni ko bayanan da ake bukata daga intanet ta kofa mai daraja 80 (Port 80). Ko kuma ince tsari ne da ke bada damar yin mu’amalar sadarwa a tsakanin Kwamfuta da shafukan intanet.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, http:// babu cikakken tsaro, don haka akwai bukatar jama’a da su kula da kyau wajan yin harkokin kasuwanci ko musayar bayanann sirri a shafin intanet wadanda basu da cikakken tsaro. Sai a kiyaye amfani da dukan katin baki a ireiren wadannan shafukan da sauran su.

Na biyu me ake nufi da HTTPS?

AMSA: Cikakkiyar Jumalar https; Hypertext Transfer Protocol Secure. Shima ya kasance kamar yadda http yake a wajan sadarwa tsakanin na’urar Kwamfuta da kuma shafukan Intanet. Amma shi wannan yana amfani da kofa mai jarajar 443 (port 443). Wannan dalili ya sanya duk wata alaakar sadarwa karkashin wannan tsari a killace take ma’ana a kewaye take da matakan tsaro masu karfi (secure).

Bugu da kari a halin yanzu duk wata mu’amalar kasuwanci ko musayar bayanan sirri anayin su ne ta wannan hanya domin magancewa da kuma toshe duk wata kofa ko baraka (back doors) da zata bada dama ga ‘yan dandatsa (Interceptors) ko masu kutse (Hackers) wadanda aniyarsu ba tagari bace.

Mai karatu zanso ka sami lokaci ka duba shafuka wadanda ake harkokin cinikayya, ko na bankuna, da na zumunta da sauran shafukan da kake amfani da su yau da kullum, zaka ga wajan adreshin su a sama akwai https://. Ko kuma da farko zai kasance http:// amma a lokacinda za’ayi biyan kudi sai ya rikide ya koma https:// domin rufe kofar da zata zama illa wajan gudanarwa. Saboda haka wannan ma mizani ne da zai tai maka wajan rage fadawa hannun mazambata a shafukan intanet.