Connect with us

Intanet

Bambancin dake tsakanin Deep Web da Dark Web

Published

on

Bambancin dake tsakanin Deep Web da Dark Web

Bambancin dake tsakanin Deep Web da Dark Web.

Wannan batu yana da matukar muhimmanci domin samun kyakkyawar fahimtar yadda tsarin intanet yake aiki lungu da sako. Akwai dumbin tambayoyi da Jama’a ke neman sanin amsoshin su. Tambayoyi kamar;

 • Menene a cikin wadannan sassa na intanet (dark web da deep web)?
 • Me akeyi da su?
 • Ta yaya ake shigar su?
 • Suna da hadari ko kuwa?

Acikin wannan rubutu nake so nayi gwargwadon kokari wajan bayyana yadda wadannan abubuwa suke. Akwai bambanci a tsakanin abubuwan guda biyu Dark Web da Deep Web amma sukan shiga cikin juna ta wasu fuskokin.

Deep Web

Sune nau’in shafukan intanet wadanda tsarin bincike na Search Engine baya iya zakulo su ko sanya su a cikin sakamakon bincike. Wato rariyar bincike bata iya ganin wadannan shafuka ballantana ta fito dasu yadda za a iya ganinsu a duk lokacin da ake bincike akan wasu al’amura, koda akwai su acikin wadannan sassa.

Hakan yana kara bayyana cewa ga duk mai son shiga shafukan intanet na Deep Web, dole ne yayi amfani da adreshin shafin (address ko link) kaitsaye ko kuma bin wani adreshi acaikin deep web din domin zuwa wani shafin ko shafuka.

Sannan kuma shafukan da ke cikin deep web sukan zamo masu amfani kwarai kamar su shafin Netflix da kuma Shafin Amazon da sauran manyan shafuka. Manyan sassan Gwamnatoci da wasu manyan cibiyoyi na intanet sukan yi amfani da wannan sashe domin tsaro.

Dark Web

Wannan kuma shine sashe mafi zurfi daga cikin deep web; wanda yafi zama boyayye ga search engines. Kuma shima dole sai anyi amfani da adreshin shafukan dake cikinsa kaitsaye, duba da yadda aiyukan ta’addanci aka fi aikatawa acin sa. Ga wasu daga cikin aiyukan da ake yadawa a cikin shafukan Dark Web.

 • Kasuwancin Mugayen Kwayoyi
 • Kasuwancin Makamai da harsasai musamman marasa rijista.
 • Yada jadawalin kayan aikin 3D ba bisa ka’ida ba.
 • Yada litattafan siyarwa ba bisa ka’ida ba
 • Gurbatattun shafuka masu ikirarin nagarta
 • Hotuna da bidiyon tsairaici musamman na Hollywood da Bollywood
 • Shafuka masu fayafayen bidiyon da ake cin zarafin yara kanana, dabbobi da zubar da jini
 • Fayafayen bidiyon tarzoma da hargitsi
 • Fayafayen bidiyon da ake lalata da yara kanana
 • Da kuma bayanai akan yadda ake sarrafa naman dan Adam
 • Kasuwar ‘yan bindiga dadi
 • Da kuma shafukan kashe rayuka wadan da sai mutum ya biya kudi kafin ya samu damar ganin wadannan munanan al’amura.
 • Dandalin ‘yan kutse a shafukan intanet
 • Matattarar Cututtukan Virus
 • Matattarar manyan ‘yan caca.
 • Dandalin yada jitajita mafi muni
 • Da sauran su…

Bugu da mafi yawancin kasuwancin da ake yi a wannan dark web din na cin amana ne. Domin babu tabbacin alkawari tsayayye. Kuma hukumomin gwamnati suna shiga suna kama mutane ‘yan ta’adda a wannan sashe na intanet duba da yadda barna tayi yawa a shafukan intanet na dark web.

Surface Web

Kafin rufe wannan makala, zan so na yi amfani da wannan dama domin bayyana Surface Web wanda shi ne sashen intanet na sarari da muke amfani dashi. Wanda ke kunshe da shafukan intanet da muke amfani da su yau da kullum kamar su; Shafukan Labarai, Shafukan sada zumunta kamar su Facebook, Twitter, Instagram da sauran su… Kuma dukkannin rariyar bincike da muke amfani dasu kamar su; Google, Yahoo, Wikipedia, Bing da sauran su kan iya ratsawa lungu da sako domin zakulo bayanai da ake nema ko ake bincike akan su.