Connect with us

Featured

Bayani akan yadda ya kamata ayi cajin batirin Komfuta

Published

on

bayani akan yadda ya kamata ayi cajin batirin komfuta

Tambayar da aka fi yawan yi ita ce ta yaya masu amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa za su ƙara wa batirinta caji, ko yadda za ka kauce wa mutuwa katsahan.

Yayin da yawancin batira ke lalacewa, wasu na tababar ko dai yadda muke amfani da su ne ke janyo mutuwarsu dungurugum, ko yadda suke riƙe cajin.

Idan haka ne ta yaya za mu yi amfani da batirin?

Bayan amfani da batiri na tsawon lokaci, yana mutuwa, masu amfani da shi na mamakin ko amfanin da suke yi da shi na kara ta’azzara lalacewarsu, ko sanya batirin yin sanyi.

Ta wani bangaren, ko za mu iya cajinsu 100 bisa 100 a ko da yaushe, ko kunna nau’arar kamar yadda ya kamata?

A wata tattaunawa da ƙwararrun kan hanyar da ta dace a yi amfani da batirin wanda yawanci ana hada su ne da ma’adinin lithium.

Tsahon lokacin da Batiri zai yi

“Fasahar yin batiri na bunkasa ne da tafiyar zamani. Shekaru goma baya, karfin batirin na’ura mai kwakwalwa samfurin laptop ya fara tabarbarewa, bayan zagayawar daruruwan yadda ake cajinsu,” in ji Ashley Rolfe, babbar jami’a a kamfanin fasaha na Lenovoda ke yankin Ireland da Birtaniya.

Batiran komfutar hannu na zamanin nan suna da ƙayyadadden lokacin amfani da su daga shekara uku ko biyar, a wannan lokacin za a iya cajinsu sau 500 zuwa 1,000.

“Kana bukatar batirin ya maka caji yadda ya dace a duk lokacin da ka sanya, na a kalla shekara uku zuwa biyar,” in ji Kent Griffith, na cibiyar binciken fasaha da ke Jami’ar Northwestern da ke Amurka, a hirarsa da manema labarai.

Ta yaya za ku iya cimma abin da kuke bukata?

Mista Rolfe na kamfanin Lenovo ya shaida wa manema labarai cewa; ”Barin komfutar hannu ta yi caji 100 bisa 100 a kowanne lokaci, yana kare batirin daga mutuwa kuma ya fi inganci ba tare da kawo matsala ba”.

Ka fi son barin kwamfiyutar hannu ta na caji a kodayaushe?

Asalin hoton, Getty Images

Komfutocin kamfanin Lenovo da sauransu suna amfani da wata na’ura da ke tabbatar da cewa batirin bai yi cajin da ya wuce ƙima ba, ko sanyata ɗaukar zafi.

Haka kuma, ”barin batirin ya yi caji 100 bisa 100, ka iya kashe ƙarfin batirin.”

Abokin aikinsa, Phil Jakes, daraktan fannin fasaha kuma babban injiniya a kamfanin Lenovo, ya amince da hakan: “Duba da yadda fasaha ta kara samuwa a shekarun nan, mun gano batiri na saurin mutuwa idan ana yawan cajinsu baki daya musamman a yanayin wuri, “.

Wasu kwararru sun bada shawarar cajin baitirin zuwa kashi 80

Asalin hoton, Getty Images

Dalili shi ne cajin batirin 100 bisa 100, shi ne abu ma fi nauyi da komfutar za ta dauka,” in ji Kent Griffith na Jami’ar Northwestern.

Kamfanin HP ya amince da haka ya kuma shaida wa manema labarai cewa: “HP bai ba da shawarar barin komfutar a caji a kowane lokaci.”

“Yawancin batiran yanzu suna da fasahar da ke kare batirin daga yin caji fiye da ƙima, kar ya kai kashi 100″, sai dai fasahar ba ta kare yawan cajin daga ragewa batirin nauyi ko sauri ko ba shi kariya daga lalacewa da wuri ba,” in ji HP.

Don haka, “idan ka rage yawan cajin batiri 100 bisa 100, akwai yiwuwar za ka dade kana amfana da shi,” in ji Griffith.

Mista Rolfe ya kara da cewa: “Batiri ya fi samun kariya idan aka yi cajinsa kashi 50, abubuwa na cunkushewa a ciki idan ya mutu baki daya ko caji 100 bisa 100.

“Domin haka kwararrun masana fasaha sun ce zai fi alfanu a bar cajin kashi 20 zuwa 80”, kamar yadda Mista. Rolfe ya yi karin bayani.

Ko da yake takaita nauyin zuwa kashi 80 yana da alfanu, amma duk da haka akwai wata tawayar ta rage karfin batari daga kashi 90 ko 95,” in ji Jakes.

Shi ma kamfanin Microsoft ya yi gargadi a shafinsa na intanet, idan an yi cajin komfutocin fiye da ƙima, zai iya rage masa ƙarko.

“Za ku iya kare batirin daga mutuwa ta hanyar caji na dan lokaci. Idan kuma dole ka bar ta a caji na tsahon lokacin ake amfani da ita, zai yi alfanu idan ka sanyata a caji.

“Idan har dole ya kasance komfutarka ta zama a kunne, ko ka yi amfani da alamar da ke takaita cajin idan ya kai wani geji, ” in ji Microsoft.

Yawancin kamfanoni kamar Microsoft, Lenovo, da HP, suna ba da damar gyara yadda kake son cajin batirinka a sashen da aka tanada domin haka.

Misali, HP na bayar da damar sanyawa a kashi 80, a wajen da za ka gyara yadda za ka kare lafiyar batirinka.

Baki daya dai idan kana son batirin ya yi karko sai ka kula da yadda kake cajinsa.

NASA ta sanyawa shalkwatarta sunan Mary Jackson, mace bakar fata kuma injiniya ta farko da ta yi aiki da su.

Ta yaya za ka kula da komfutarka ta hannu?

Amma wannan ba yana nufin za ka yi gaggawar kashe cajin wayarka da zarar ya kai kashi 100 ba.

Idan ba ku da wutar lantarki za ka iya tafiya da kwamfiyutar hannu da abin cajinta

Asalin hoton, Getty Images

Amma duk da haka “a dan tsakanin nan batira na da ƙarko a wannan lokacin, wanda ba abun damuwa ba ne ga wasu mutane.”

A karshe Mista Rolfe’ ya ce abu muhimmi shi ne ka yi tunanin kan yadda za ka yi amfani da komfutarka.

Tabbatar batirin ya yi caji yadda ya kamata. Ta wani fannin dole ka samu wutar lantarkin da za ka dinga cajin. Amma mafi alfanu shi ne yi mata cikakken caji ba lallai sai ka na bukatar amfani da ita ba.

Tushen Labari

 

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku