Connect with us

Darasi

Cigaban darasin kwamfuta akan software

Published

on

manhajoji-masu-bukatar-intanet

Cigaban darasin kwamfuta akan software

Mu’amalar yau da kullum da akeyi da na’urori, akwai bukatar manhajoji domin aiwatar dasu. Akwai manhajoji masu yawa musamman na Kasuwanci da sauran aikace-aikace kama daga wadanda ake amfani da su wajan tattaunawa kaitsaye, da kuma wadanda ake lissafi, hasashe, kididdiga, kasafi, gyaran hoto,  gyaran sauti da sauran su…

Su wadannan manhajoji akwai wadanda an tsara su ne domin suyi aiki akan kwamfuta ko wayoyi kawai. Wato babu bukatar hada na’ura da tsarin sadarwa na intanet. Su ake kira a turance DESKTOP APPLICATIONS SOFTWARE. Akwai bukatar a saka su (install) a na’ura ta hanyar amfani da paipan CD ko wata hanyar mafi dacewa, kafin har a sami damar amfani dasu kamar yadda nayi bayani a sama.

Haka kuma akwai wadanda aka tsara su dole sai an hada na’ura da intanet sannan za’a iya amfani da su. Su kuma ana kiran su WEB-BASED APPLICATION SOFTWARE. Su kuma wadannan ba sai an saka su a na’ura ba. Ana amfani da manhajar watayawa a intanet (Internet Browser) domin samun damar yin aikace-aikace da su. Kuma dole sai da alaakar sadarwar intanet (internet connectivity) sannan za suyi aiki.

Wannan tsari ya kawo cigaba sosai ta yadda aka samu raguwar cinkoson kayan aiki a Kwamfuta da kuma hadarin lalcewar kaya saboda cututtukan na’ura (Virus and co.) ko sulwantar na’uara gaba daya. Saboda komai yana intanet karkashin kulawar masana ta hanyar amfani da manyan rumbunan dana kayan aiki (Cloud Storage), wadanda manhajoji ne masu basira (software-based) suke basu kulawa ta fuskar tsaro da sauran su.