Connect with us

Darasi

Cigaban Darasin Kwamfuta na 4 akan Utility

Published

on

Manhajar-Garambawul

Cigaban Darasin Kwamfuta na 4 akan Utility

Kamar yadda bayanai suka gabata cikin darussan baya, maqala akan manhaja tana da fadin gaske. Domin akwai na’ui-nau’i na manhajoji masu yawa, saboda yadda manhaja ta zamo ginshiki wajan tafiyar da aiyukan kwamfuta da dange-dangen ta.

Wannan manhaja samfurin utility ta kasance reshe daga cikin manhajar gudanarwa da sarrafa kwamfuta (System software), wadda muhimmin aikinata shi ne yin garambawul a na’urar kwamfuta da sauran na’urori masu aiki kamar kwamfuta.

Ana amfani da manhajar utlilty domin gudanar da garambawul ta fuskoki masu yawa, domin inganta aikin kwamfuta kamar su; karin sauri, share duk wasu tarkace marasa amfani daga cikin kwamfuta, samar da tsaro, daidaita mu’amala tsakanin sassan hardwar da software, binciko matsaloli da mangance su, da sauran su…

Ga kadan daga misalan manhajojin garambawul:

  • File Viewer: Wannan manhaja tana aiki a lokacin da aka bukaci bude wani aiki ko wasu bangarori kamar su files da kuma Folders. Windows explorer shi ne misalin file viewer.
  • File Compressor: Wannan kuma ana amfani da ita wajan matse aiyuka kamar file ko folder domin rage girman su. Misali; Winrar, WinZip da sauran su…
  • Diagnostic Utilities: Wadannan ana amfani da su domin gano matsala da mangance ta musamman ga hardware da kuma software. Suna da adadi mai yawa dangane da nau’in manhajar sarrafa kwamfuta (OS).
  • Disk Scanner: Wannan manhaja tana da matukar amfani a kwamfuta saboda tana aiki wajan gudanar da gyare-gyare ga babban rumbun adana kayan aiki na dindindin (Hard Disk Drive).
  • Antivirus: Manhaja ce dake bada tsaro ko kariya ga na’urori abisa illolin cututtukan na’ura wato virus da dangee-dangen su… tana bincika kwamfuta domin ta zakulo cutar virus domin magance ta. Haka kuma tana hana sabuwar cutar shiga cikin kwamfuta, matukar ana sabuntawa akai-akai (regular update).
  • Disk Defragmenter: Wannan manhaja tana da alaka da rumbun adana kayan aiki (Hard Disk Drive) da kuma kayan aikin da ake adanawa a cikinsa (files da folders). Yakan tattara kaya waje guda domin kara fadi ko girman sarari (empty space) a cikin rumbun.
  • Backup Utility: Wannan manhaja tana taka muhimmiyar rawa wajan magance matsalolin sulwantar kayan aiki ko munimman bayanai. Ana amfani da ita wajan yi kopi na dukkan kayan aiki ko muhimman bayanai, sannan a adana su a wani waje. Aknyi amfani da ita wajan dawo da kayan aiki ko bayanan da aka rasa.
  • Data Recovery Utility: Haka zalika wannan manhaja ana amfani da ita wajan dawo (restore) da kaya ko bayanan da suka lalace (damaged) ko suka gurbata (corrupt) a bisa dalilin daukewar wutar lantarki a lokacin da ake tsaka da aiki da kwamfuta.

Kadan kenan daga cikin misalan manhajar gudanar da garambawul (Utility Software). Kuma akan same su kunshe a cikin manhajar sarrafa na’ura (operating system). Bayan haka akwai wadanda ake iya sakawa daga baya, sabanin wadanda suka zo a cikin (OS).

Continue Reading