Connect with us

Darasi

Cigaban darasin Kwamfuta na uku – Software

Published

on

manhajar-aiki

A darasin jiya na kare bayani akan nau’in Manhajar Sarrafa Na’ura wato OPERATING SYSTEM. Yanzu zan dora daga inda na tsaya. Dafatan Allah ya amfanar damu baki daya.

(2) APPLICATION SOFTWARE

Kamar yadda muka fahimta a cikin karatuttukan mu na baya cewa na’urar kwamfuta tana aiki ne bisa umarni (instructions, software ko programme). Haka kuma antsara Kwamfuta yadda za’a iya yin aiki da ita a kowanne fanni na aikace-aikace yau da kullum, ta hanyar amfani da manhajoji  wadanda aka tsarasu rukunni-rukunni yadda za’a iya yin aiyuka mabambanta dasu. Wadannan manhajoji sune Application software.

Kuma ana saka su (install) ne a na’ura bayan an saka manhajar sarrafawa (OS). Hakan yana bayyana cewa babu yadda za’ayi a saka manhajar aiki a na’ura ba tare da ana saka manhajar sarrafawa ba.

Ga misalan Manhajar Aiki nau’i – nau’i

  • Word processing software: wannan manhaja ce da ake amfani da ita wajan rubuce-rubuce kamar wasika, littafi, labarai, aikin ofis dama kowanne irin rubutu domin tsarwa, ingantawa da kuma adanawa domin kowanne lokaci, misalin su; Microsoft Word, Microsoft Works, AppleWorks da sauran su.
  • Spreadsheet Software: ana amfani da wannan manhaja domin lissafi kamar hasashe, kasfin kudi, kananan lissafi da manya musamman aikin aikin banki, misalin su; Microsoft Excel, Quattro Pro, Lotus 1-2-3, MS Works da sauran su…
  • Desktop Publishing Software: ana amfani da wannan manhaja wajan tsarawa da kawata aiyukan hotunan talla (banner), Katinan gayyata da na taya murna (invitation & gifts cards), allunan talla (signs), jarida da litttafai da sauran aiyuka, misalin su; Microsoft Word, Microsoft Publisher, Adobe PageMaker da sauran su…
  • Database Software: Ana amfani da wannan manhaja wajan tsarawa da adana muhimman bayanai na Ma’aikata ko Dalibai da sauran su, kundin adreshin ‘yan kasa. Matattarar bayanai domin samun saukin tsarawa da kuma saukin bincikawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Misalin su; Microsoft Access, FileMaker Pro da sauran su…
  • Communication Software: wadannan kuma manhajoji ne dake da ruwa da tasaki wajan hada alaaka tsakanin na’urori domin sadarwa a tsakanin su ta hanyar sauti, bidiyo, ko tattaunawa kai tsaye (chat) da saunra su. Misalan su; Microsoft Net Meeting, IRC, ICQ da sauran su…
  • Presentation Software: ana amfani da wannan wajan tsara laccar a tarurruka ko kawata hotuna masu juyawa da kansu (slideshow), kuma ana iya chakuda hotuna da sauti domin kayatarwa. Misalin su; Microsoft PowerPoint, Camtasia da sauran su…
  • Internet Browsers: ana amfani da wannan manhaja domin bincike, watayawa, aikawa da karbar sakonni (email) dama sauran aiyuka masu yawa duk a intanet. Misalan su; Moxilla Firefox, Chrome, Opera, Microsft Internet Explorer da sauran su…
  • Email Programs: suma wadannan ana amfani dasu a rayuwar yau da kullum wajan aikawa da karbar sakonni ta intanet wato email. Misalan su; Microsoft Outlook, Netscape Messenger, AOL Browser, Gmail, Yahoomail da sauran su…

Akwai misalan manhajojin aiyuka masu yawan gaske, wadanda suka hada da su Corel draw wadda ake amfai da ita wajan tsara katinan shaidar aiki, kalanda, mujalla, bajo da sauran su. akwai Photoshop wadda ake amfani da ita wajan gyara hotuna, sauyawa hotuna fasali ko kara musu kyau. Akwai wadanda su na nishadi ne kamar na wasanni (games) da kuma na kallon pinapinai (Players) da sauran su. Akwai Microsoft Office wanda ya kunshi manhajoji da yawa kuma na bayyana wasu daga cikin su a can sama.

Wadannan manhajoji ana amfani dasu daida bukatar mai amfani da na’uarar kwamfuta ko wayoyin zamani (Smartphones).

Mu hadu a cigaban karatu…

Continue Reading