Connect with us

Manhaja

Computer: Bambanci tsakanin Update da Upgrade

Published

on

Computer: Bambanci tsakanin Update da Upgrade

Computer: Bambanci tsakanin Update da Upgrade

Wannan tamabaya ce, dake neman cikakken bayani domin samun kyakkyawar fahimta a tsakanin wadannan al’amura guda biyu, masu muhimmanci a duniyar fasaha. Kowanne daya daga cikin su yanada matukar muhimmanci kuma suna taka rawa wajan inganta aikin Kwamfuta da sauran na’urorin da muke amfani da su domin samun saukin gudanar da aiyukan yau da kullum.

Hakika babu wani bambamnci mai girma a tsakanin su, duba da yadda a kowanne lokaci za’a iya amfani da kowannen su wajan bayyana matakin ingantawa da kulawa ga dukkan sassan na’urar Kwamfuta da sauran na’urori a kowanne bigire na aiki. Amma duk da haka zanyi bayani akan yadda zamu fahimci yadda kowannen su ke taka rawa.

Update shi ne wanda ake nufi da sabuntawa daga tsohon al’amari zuwa sabon al’amari. Misali; manhajar sarrafa kwamfuta (Windows operating system), wanda akan sabunta wasu daga cikin sassan manhajar, musamman bangaren tsaro domin toshe kofofin da za aiya kutse ko satar bayanan sirrin masu amfani da manhajar. Wanda kwamfuta kanyi downloading din su idan akwai sadarwar internet akai. ko kuma manhajar Anti Virus wadda itama takan yi updating a duk lokacin da aka sabunta manhajar daga kamfani.

Upgrade kuwa yana nufin daga darajar sassan na’ura. Wanda kacokam aka cire tsohon al’amari ko karami a musanya su da sabon al’amari ko babba. Misali; musanya karamin rumbun ajiya (Hard Disk Drive) na kwamfuta mai giraman 100GB zuwa babba mai girman 500GB. Ko RAM daga 2GB zuwa 4GB. Har kullum upgarde yana tattare da cirewa da sakawa (replacement) musamman ga sassan kwamfuta da sauran na’urori. Ko kuma kari akan waanda ake aiki da shi

Bugu da kari, kowanne daga cikin su yana inganta yadda na’uara ke gudanar da aiki. Akan sami damar yin update a kyauta musamman idan ya kasance ana amfani da manhaja wadda aka siya da kudi (Premium ko Full Version) a duk lokacin da kamfani ya sabunta manhaja. Amma upgrade ba kyauta bane, tunda a kwai bukatar cirewa da sakawa, kamar yadda na bada misali a can sama. Kuma akanyi amfani da kalmar Patches (Gyara ko karin armashi) a maimakon Updates.

Ku kasance da wannan shafi domin samun bayanan Fasaha a kowanne lokaci. Ku ma zaku iya bada taku gudummawar a kowanne fanni na kimiyya da Fasaha.