Connect with us

Shafukan Zumunta

Coronavirus: A yanzu ne Facebook ke da matukar muhimmanci a duniya

Published

on

Shafin-Facebook

A yanzu ne Shafin Facebook ke da matukar muhimmanci a duniya. Idan muka yi la’akari da yadda annobar korona ke daukar rayukan al’aumma a kasashen duniya, da kuma yadda dokar zaman gida, da bada tazara tsakanin al’umma domin gujewa cigaban yaduwar cutar korona, wanda hakan ya dakatar da al’amura masu yawan gaske. Kuma akwai bukatar aiwatar da su domin cigaban rayuwar mu ta yau da kullum.

Fasaha tana taka muhimmiyar rawa a wannan lokaci na kauracewa cudanya da juna a kowanne bigire. Amma akwai abubuwa da suka zama dole a gudanar da su musamman aiyukan da Addinai suka tanadarwa mabiyan su. Shuwagabannin addinai na duniya suna shan matsain lamba akan dakatar da dukkan tarurrukan ibadah saboda gujewa yaduwar annobar korona. An dakatar da Sallar jam’i a masallatai, da kuma majami’u na kiristoci da sauran su…

Wannan dalili ya sanya Facebook fadadawa da kuma bijiro da sababbin gurabe domin bawa mabiya addinan damar cigaba da aiwatar da dukkan mu’amalar su ko tattaunawa akan abinda ya shafi cigaban addinan a fadin duniya baki daya.

Ana sa ran wannan yunkuri na facebook zai taimakawa kungiyoyin addinai ta fuskar cigaba da tarurrukan su ta shafin facebook ba tare da yin mu’amala ta zahiri ba. Kuma za’ayi ta amfani da su har zuwa karshe da bayan wannan annoba ta coronavirus.

Daga cikin abubuwan da mabiya addinai zasu yii amfani da su domin cigaba da gudanar da al’amaura a wannan lokaci na barkewar annobar coronavirus kamar yadda aka saba sun hada da;

  • Facebook Pages: Za a iya bude shafi na musamman a facebook domin cigaba da gudanar da al’amuran addini, za a iya yada abubuwa masu muhimmanci na fadakarwa, ilimantarwa da wa’azantarwa, har da tattaunawa akan al’amura masu bukatar shawarwarin jama’a kafin tsayar da manufa daya.
  • Facebook Groups: Haka shi ma group na facebook zai taka muhimmiyar rawa wajan hada kan al’umma wadanda suke da fahimta iri daya. Za su iya yada dukkan abubuwan cigaba a tsakanin su ta wannan hanya kamar yadda aka saba. Kuma a kwai bambanci wajan yadda ake yada abubuwa a tsakanin page da group.
  • Facebook Events: Shi ma wannan zai taka muhimmiyar rawa, musamman idan akayi amfani da shi wajan gudanar da tarurruka domin gudanar da aiyukan addini. Za ayi cudanya da juna ta hanyar fasaha ba tare da yin cudanya ta zahiri ba.
  • Utilising WhatsApp: Kuma za’a iya amfani da wannan manhaja wajan isar da sakonnin da ma yadawa cikin sauti, misali; karatun al’qurani, hadisai da jawabin malamai da sauran al’amura masu muhimmanci duk atsakanin wadanda ke cikin group kamar yadda aka saba a kowanne lokaci.
  • Watch Party: Za a iya tsara lokuta domin tarayya wajan kallon fayafayen bidiyo na ilimi ko na fadakarwa har ma da jawaban manyan malamai ko dalibai domin kallo da sauraro tare. Kuma za’a iya tattaunawa kai tsaye domin bada gudummawa, shawarwari ko jin ra’ayoyin kowa akan abubuwanda aka karu da shi.
  • Facebook Live: Za a iya amfani da wannan hanya wajan nuna hoton bidiyo kai tsaye ta facebook, jawabin wani babban malami, ko dalibi, ko masana a fannoni daban-daban na addini domin gabatar da lacca, wa’azi, tafsiri ko wasu misalan yadda akae gudanar da aiyukan addini a ikace. Hakan zai bada dama ga al’ummomi dake gida samu damar kallo, da kuma samun damar tofa albarkacin bakunan su (comments) akan abubuwan da aka tattauna a bidiyon, da kuma kara yada shi zuwa ga wasu ‘yan uwa da abokan arziki.

Bugu da kari Daraktan Facebook na yankin Africa ya kara jaddada cewa a wannan lokaci na barkewar annobar covid-19 facebook ya dukufa ka’in da na’in wajan bijiro da sababbin hanyoyin da kuma inganta wadanda ake amfani da su tuntuni domin al’umma su amfana wajan zaman gida saboda annobar corona virus.