Connect with us

Barkatai

Coronavirus: Amfani da fasahar zamani zai karu a cikin watan ramadan 2020

Published

on

Coronavirus: Muhimmancin fasahar zamani a cikin watan ramadan 2020

Coronavirus: Amfani da fasahar zamani zai karu a cikin watan ramadan 2020

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Barkan mu da ganin wannan lokaci na, mai tarin albarka na azumin watan Ramadan a shekarar 2020. Hakika azumin wannan shekara yazo wa musulmin duniya a cikin wani yanayi mara dadi. Duba da yadda dukkan aiyukan musulunci da aka saba gudanarwa cikin taro ko Jam’i, kama daga sallar juma’a zuwa makarantu duk anrufe su. Hakan ya biyo bayan bullar annobar corona.

Wannan annobar corona ta zamo sular sulwantar rayukan mutane masu yawa a fadin duniya. Wadda haryanzu tana cigaba da ta’annati a kasashen duniya. Matakin da aka dauka a duniya domin dekile cigaban yaduwar cutar sun hada da; Yanke musabaha tsakanin jama’a, Bada tazara tsakanin jama’a yayin haduwa wajan gudanar da wasu aiyuka, Hana cudanya ko taro a tsakanin al’umma, wanke hannu, toshe hanci, takaita zurga-zurga da sauran su…

Fasaha ta kawo sauye-sauye a duniya wajan gudanar da al’amura cikin sauki da sauri. Ta shiga kowanne lungu da sako na rayuwa, ta zamo jigo a rayuwar al’aumma. Kuma kullum kara fito da sababbin abubuwa akeyi domin kara ingatawa da saukaka fahimta wajan gudanar da aiyuka a tsarin fasaha. Tuntuni kafafen sada zumunta sun zamo zaurukan tattauna al’amura masu matukar muhimmanci ga rayuwar al’umma baki daya. Akwai manhajoji da shafukan zumunta masu tarin yawa da musulmi zasu iya bude zauruka ko dandali wanda za’ayi tarayya domin yada kalamai wadanda aka saba a dukkan ramadan da suka gabata.

Saboda haka a wannan yanayi da duniya ke ciki na annobar korona, da kuma takaita mu’amala tsakanin al’umma yasa nake amfani da wannan dama wajan kara fadakar da al’umma akan muhimmancin da fasahar zamani ke dashi wajan cigaba da sada zumunci, fadakarwa, ilimantarwa da tunatarwar da aka saba yi a lokacin watan ramadan ta hanyoyi daban-daban, a cikin wannan ramadan na 2020 da muyi amfani da shafukan intanet wajan yada al’amuran addini da kalamai masu tsada masu lada ga ‘yan uwa da abokan arziki na duniya baki daya kamar yadda aka sabayi a kowanne ramadan kafin zuwan wannan na 2020.

Malami da dalibai sukan yi tunatarwa akan abubuwa kamar haka; Addu’o’in da yakamata musulmi ya lazimta cikin watan ramadan tundaga farko har zuwa karshen sa, Hadisai a kowacce rana, hanyoyin masu sauki wajan haddar alqur’ani cikin watan ramadan, yada karatun tafsiri ta manhajoji da shafukan intanet, gaishegaishen buda baki, hanyoyin tuba da istigfari da sauran su…

Wadancan dalilai suka sanya azumin ramadan na shekarar 2020 ya zamo na daban, wanda ba’ataba samun irin sa ba a tarihin duniya. Addinin musulunci ya yi bayani akan kowanne irin al’amari da kuma yadda za’a magance kowacce irin matsala, masifa, ko annoba dake addabar mutane a fadin duniya. Dan haka addu’a tana da matukar tasiri

Ubangiji Allah ya datar damu da dukan alkhairai da falalar dake cikin wannan wata na ramadan. Allah ya kare mu daga wannan annoba ta corona, ya yaye mana ita daga doron kasa baki daya.

RAMADAN KAREEM!!!

Continue Reading