Connect with us

Manhaja

Coronavirus: Kamfanin Zoom ya gaza wajan bada cikakken tsaro ga masu amfani da manhajar sa

Published

on

Kamfanin manhajar zoom ya gaza

Kamfanin Zoom ya gaza wajan bada cikakken tsaro ga masu amfani da manhajar kamfanin.

Bincike ya bayyana cewa ‘yan ta’addan intanet sunyi nasarar sace bayanan sirri fiye da dubu dari biyar (500,000) daga shafi da manhajar Zoom wadda kamfanoni, ma’aikatu da manyan makarantu ke amfani da su wajan gudanar da aikace -aikace daga gida (Video Conferencing), musamman a wanna lokaci na annobar coronavirus.

Sanini kowa ne a wannan shekara an samu barkewar annobar coronavirus (Covid-19). Kuma hanyar dakile cigaba da yaduwar wannan annoba shi ne, kauracewa dukkan tarurrukan jama’a.Wanda haka ya jawo amfani da fasahar zamani domin cigaba da gudanar da al\amura kamar yadda aka saba musamman a kasashen da annobar tafi yin illa.

Kamfanin manhajar Zoom, yayi shuhura a fannin fasahar tattaunawar nesa da juna tareda ganin hoton kowa a lokacin tattaunawa (Video Conferencing).

‘Yan ta’addan intanet sunyi nasarar sace bayanan sirri wadanda masu amfani da manhajar Zoom ke amfani dasu wajan login (username da password). Kuma bisa al’adar wannan manhaja ana amfani da adreshin email madadin username. Wadannan ‘yan ta’adda suna siyar da wadannan bayanai akan kudi kalilan koma sunyada su kyauta a cikin yanar gizo mai duhu (dark web).

Mafi yawancin bayanan da akayi nasarar sace su na kamfanoni ne, manyan Jami’o’i (Florida da Colorado) da kwalejoji har da manyan bankuna dake kasar amurka kamra su Citi Bank da Chase. “yan ta’addan sun fara siyar da bayanan sirrin a dark web tun 1 gawatan Afrilu.

‘Yan ta’addan da sauran jama’a wadanda suka sami wadannan bayanai na sirri a intanet suna amfani dasu wajan yin kutse a lokacin da kamfanoni, jami’o’i da sauran su ke tsaka da amfani da tsari ko manhajar zoom inda suke tura sakonni marasa amfani, kamar na batsa ko cin mutunci.

Sugaban kamfanin Zoom, Eric Yuan, ya magantu akan wannan batu inada ya bada hakuri ga abokan huldar kamfanin musamman wadanda abin yafi shafa.

Babbar illa da tafi addabar mutane wadda kuma nasarace ga ‘Yanta’adda ita ce, mafi yawancin jama’a suna amfani da password guda daya ne a kowanne bigire a intanet. Wanda hakan yanada matukar hadari ga sirrinkan jama’a masu gudanar da dukkan al’amuran su a intanet musamman a wannan lokaci na annobar corona.