Connect with us

Fasaha

Coronavirus: ‘Yan ta’addan intanet suna damfarar mutane miliyan 18 kullum

Published

on

sakonnin email

‘Yan damfara na aika sakonnin email miliyan 18 kowace rana kan cutar korona, ga masu amfani da Gmail, a cewar kamfanin Google.

Kamfanin fasahar ya ce annobar ta janyo karuwar damfara ta intanet sosai inda ‘yan damfarar ke dabarar samun bayanai masu muhimmanci daga wurin mutane.

Kamfanin ya ce yana rufe adireshin email miliyan 100 kowace rana wadanda ake amfani da su wajen damfara.

A makon da ya gabata, kusan kashi daya cikin biyar na sakonnin email da aka tura na damfara ne da suka danganci cutar korona.

A iya cewa cutar a yanzu ita ce jigon damfara mafi girma, in ji kamfanin.

Mutum biliyan 1.5 ne ke amfani da adireshin email na Google wato Gmail.

Ana aika wa mutane dumbin sakonnin email kala-kala da ke nuna kamar daga hukumomi suke, akamr hukumar lafiya ta Duniya (WHO), a wani yunkuri na jan ra’ayin mutane su sauke wata manhaja ko kuma su bayar da gudumowa ga wani shiri na karya.

Cigaban karatu…

Continue Reading