Connect with us

Manhaja

Corornavirus: An kara yawan mutane a video calls na whatsapp

Published

on

An kara yawan mutane a video call na whatsapp

An kara yawan mutane wajan gudanar da video calls a manhajar whatsapp, daga matakin mutane 4 zuwa 8. Kamar yadda kamfanin Facebook wanda shi ne mamallakin manhajar WhatsApp ya alkawarta a baya-bayannan.

Bukatar amfani da fasahar video calls ta karu matuka a wannan shekara musamman a yanayi da duniya ke ciki na mamayar annobar corona virus. Ma’aikatun Gwmnati da masu zaman kan su, Masana’antu, Makarantu da sauran matattarar Jama’a duk anrufe su domin dakile yaduwar cutar a sassan duniya. Wanda hakan ya zamo koma baya a duniya baki daya ta fuskar cigaban dukkanin al’amuran rayuwar al’umma ta yau da kullum.

A cikin wannan yanayi fasaha ce ta ke taka rawa wajan samar da hanyoyin cigaba da gudanar da dukkan al’amura daga ko’ina, ba tareda anyi cudanya ta zahiri ba. Haka zalika dukkan hanyoyin sadarwa da nahajoji akwai bukatar tsaurara matakan tsaro a kansu duba da yadda barazanar kutse ta karu a wannan lokaci. Wanda hakan ya haifar da matsaloli ga wasu manyan manhajojin da aka saba amfani da su wajan gudanar da video conferencing suka sami matsalar kutse a wannan lokaci na zaman gida.

Manahajar WhatsApp tayi shuhura a duniya a kowanne fanni na rayuwa ana amfani da shi wajan musayar sakonni da kuma yada abubuwa masu amfani a tsakanin al’umma. Saboda haka whatsapp ya kara samun tagomashi daga wajan al’umar duniya musamman a wannan lokaci na kulle saboda cutar corona.

Kamfanin Whatsapp ya sha kiraye-kiraye musamman akan bukatar karin yawan mutane da su iya tattaunawa ko gudanar da taro kai tsaye kuma suna ganin juna (Video calls ko Video conferencing) daga mutane hudu zuwa mutane da yawa. To amma kanfanin ya yi iya kokarinsa a wannan lokaci ya kara mutane hudu akan hudun farko, wanda hakan ya sanya mutane takwas zasu iya video calls a ta ke. Wannan kari ya shafi sabuwar manhajar whatsapp na Android da kuma na iOS. Haka zalika kowa zai iya sabunta wadda ta ke kan wayarsa domin samun damar amafana da wannan cigaba.

A duk lokacin da mutum ke bukatar amfani da wannan tsari, zai yi amfani da alamar kan alamar kan wayawaya dake sama a shafin group na whatsapp. Idan aka danna wannan alamaalamar kan waya zai bude shafin da ke dauke da Sunaye ko lambobin mutanen da cikin group din, daganan sai danna suna ko lambar wanda ake so ayi video calls din akalla mutane takwas (8).  Kwararru a fannin tsarawa na manhajar whatsapp sun sanar da cewa aikin kara yawan jama’a a fuskar kowacce irin waya ba abune mai sauki ba , idan akayi la’akari da tsarin fuskar (screen)  wayoyin zamani. Dan haka a wannan lokaci sunyi nasarar raba screen din gida takwas yadda kowanne gurbi zai iya nuna hoton bidiyo a lokacin tattaunawa tsakanin al’umma.

A karshen, kamfanin WhatsApp yana aikin fadada manhajar yadda zata kasance tana aiki akan kowacce irin waya a fadin duniya baki daya.

Ku kasance da wannan shafi na Duniyar Fasaha Online a kowannan lokacin domin samun sababbin al’amura na cigaba a fannin Kimiyya da Fasaha na Zamani.

Continue Reading