Connect with us

Manhaja

Covid-19: Kamfanin WhatsApp ya kara tsaurara matakan tsaron sadarwa

Published

on

Covid-19: Kamfanin WhatsApp ya kara tsaurara matakan tsaron sadarwa

Kamfanin WhatsApp ya kara tsaurara matakan tsaron sadarwa musamman ga tsarin kira (WhatsApp & Video Calls). Duba da halin da dukkan al’amura suka tsinci kansu a wannan lokaci da annobar corona ta mamaye duniya. Kimanin mutane bilyan biyu (2 billion users) ke amfani da manhajar whatsapp a duniya.

Akwai manhajoji masu yawa da ake amfani da su wajan sadarwa da tattaunawar kai tsaye tare da ganin juna (Tele & Video Conferencing) amma sai ya kasance akwai rauni waja matakan tsaro. Misali manhajar ZOOM wadda kusan ita ce kan gaba wajan gudanar da aikyuka, karatu da sauran al’amura daga gida. A wannan lokaci da annobar corona ta hana mu’amala ta zahiri tsakanin al’umma, saboda haka akwai bukatar kara matakan tsaro ga hanyoyi da manhajojin sadarwa irin wadannan.

Gwamnatin kasar amurka ta kara matsin lamba ga kafafen sadarwar zamani da su kara inganta matakan tsaron manhajojin su domin toshe marakar da ‘Yan ta’addan intanet ke amfani da su wajan cimma burin su na kutse da satar bayanan sirri na jama’a masu amfani da su musamman a lokaci mai tsauri da ake ciki yanzu a duniya baki daya.

Wadannan dalilai suka sanya kamfanin manhajar WhatsApp zage damtse wajan kaiwa gaci fiye da kowacce manhaja mai aiki iri nata, wajan killace dukkanin sadarwa tsakanin mutane (end-to-end encrypted) ba tareda su kamfanin ko wanin su ya datsi bayanan da ake tattaunawa ba, ta kowanne sashe kama daga: tattaunawa ta kaitsaye (Chat), Kiran waya (WhatsApp Calls) da kuma kiran waya tare da ganin juna (WhatsApp Video Calls).

Bangaren Video Calls na manhajar WhatsApp shi ne ake da bukatar kara bunkasa shi, tunda shi ne ya maye gurbin mu’amala ta zahiri tsakanin jama’a, domin rage karfin yaduwar annobar corona. Wanda a halin yanzu mutane hudu (4) ne kawai zasu iya tattaunawa kaitsaye tare da ganin juna. Kuma shi aka fi bukata yanzu a duniya domin cigaba da gudanar da al’amura kamar yadda aka saba kama daga; aikin ofis, fannin ilimi, kasuwanci da sauran su…

Manhajar WhatsApp kan sanar da jama’a a kowanne lokaci cewa, dukkan tattaunawar dake gudana a killace ta ke (Messages to this chat and calls are now secured with end-to-end encryption).

 A halin yanzu kusan dukkanin sauran manhajoji kowa ya dukufa wajan karawa hanyoyin sadarwar su karfin matakan tsaro domin kare sirrin masu amfani da manhajojin na su, kamar Micrsoft da ma’aikatan su, Skype, Facebook messenger da sauran su… Kasancewar suma akwai dumbin jama’a masu amfani da su.

Duk da wannan yunkuri da kamfanin manhajar whatsapp ya yi ba zai girgiza kasuwar manyan kamfanoni kamar su Zoom da Kuma Microsoft ba wadanda sukayi shuhura a fagen Video Calls ba. Amma dai karfafa matakan tsaro shi ne matakin farko da ake bukata ga kowacce irin manhaja musamman a wannan lokaci da mu’amalr zahiri tsakanin al’umma ta zamo barazana ga rayuwa.