Connect with us

Fasaha

Covid-19: Kamfanonin Apple da Google na kokarin samar da tsarin gano masu cutar corona

Published

on

Kamfanonin Google da Apple

Covid-19: Kamfanonin Apple da Google na Kokarin samar da tsarin gano masu dauke da cutar coronavirus.

Wannan batu ya taso ne duba da yadda annobar corona ke dibar rayukan jama’a a kasashen Duniya. Kuma wannan batu ya samu karbuwar da har aka kulla alaaka tsakanin manyan kamfanonin Fasaha na Duniya wato Apple da Google domin samar da manhajar da zata aiki akan wayoyin zamani (Smartphones).

Kasar Singapore ma tace baza abarta a bayaba wajan kaddamar da wannan manhaja mai suna “Contact-Tracing” manhajar da zatayi kara domin ankarar da mutum cewa yana kusa ko da wanda ke dauke da cutar coronavirus.

Wannan hadin gwiwa zai samar da tsari a cikin manhajar sarrafa wayoyin smartphone na kamfanin Apple; iPhones da sauran su… da kuma na Kamfanin Google; wato Android wanda sabon tsarin zai basu damar musayar bayanai ta hanayar fasahar Bluetooth.

Covid-19: Kamfanonin Apple da Google na Kokarin samar da tsarin gano masu cutar corona

Kamfanonin guda biyu sun bayyana cewa wannan shine karo na farko da suka hadu domin samar da wani babban al’amari domin taimakawa Duniya wajan yaki da wannan annoba ta cuta ta corona.

Wannan babban yunkuri ya hada da hasalewar Gwamnatocin kasashe wajan amfani da fasahar gano matsayar mutum a doron kasa (GPS) wajan gano masu dauke da cutar domin dakile cigaban yaduwar cutar. Sannan kuma za a bada kulawa ta musamman wajan killace bayanan sirri na jama’a (Privacy). Shugaban kasar Amurka Donald Trump a lokacin da yake tofa albarkacin bakin sa akan hadin gwiwar kamfanonin guda biyu ya bayyana cewa lallai zasu yi duba na musamman akan al’amarin.

Kamfanonin guda biyu sun tabbatar da cewa Bayanan Sirri, da sauran bayanan jama’a na alamuran yau da kullum sune matakan farko da zasu fi bawa fifi ko wajan tsaro a wannan tsari. Wanda hakan shine zai bawa jama’a damar sakin jiki da kwanciyar hankali wajan amfani da manhajar.

Manhajar zata aika da sakamako ga cibiyoyin da aka tsara ta hanyar sadarwar zamani domin ayi gaggawar daukar matakin killace masu dauke da cutar. Hakan zai zamo babbar hanya wajan magance yaduwar cutar coronavirus a duniya baki daya.