Connect with us

Fasaha

Dakta Pantami ya bada shawarar hada rijistar layin waya da katin dan kasa har da BVN

Published

on

Dakta Isa Ali Pantami

Dakta Pantami ya bada shawarar hada rijistar layin waya da katin dan kasa har da BVN

Ministan sadarwa Dakta Isah Ali Pantami yayi kira ga sababbin mambobin hukumar gudanarwar hukumar sadarwa ta kasa  da su hada rajistar sababbin layukan wayoyi da bayanan katin dan kasa da lambar banki ta BVN.

Pantami wanda yayi kiran yayin kaddamar da hukumar gudanarwar NCC a Abuja yace yana da matukar muhimmanci a dauki wannan mataki domin ya dace da tsare tsaren gwamnati mai ci.

Yace shirinsu shine sanya ido kan layukan wayoyi miliyan 9 da dubu dari 4, da wadansun su basu da rijista yayin da wasu rijistarsu ba ta kammala ba.

Dakta Pantami ya bada shawarar cewa kada wani mutum ya mallaki layukan waya sama da uku ba tare da wani kwakwkwaran dalili ba.

Ya bukaci mambobin hukumar gudanarwar NCC dasu jajirce tare da yin aiki tukuru wajen cimma muradan da aka sa a gaba.

Continue Reading