31 C
Kano
Thursday, October 22, 2020

Dalilan da ke sanya rana yin ja a wasu lokutan

Mafi Shahara

Hakikanin abin da ke faruwa sananne ne, amma kun san dalilin da ya sanya hakan ke faruwa?

Kun fi ganin hakan a lokacin da rana ta fito ko ta fadi.

Rana kan sauya launi zuwa ja, sannan sararin sama ya yi rawaya-rawaya, toka-toka ko ma shuɗi-shuɗi mai duhu.

Yanayin kan nuna kamar karin waƙe da annashuwar soyayya, suna ta motsawa.. sai dai mafi a’ala kan haka, shi ne, tsantsar kimiyya

Duba a ƙashin kanka, amma ka tuna ka da ma ka kalli rana kacokam kai tsaye!

Kuma ka da ka yi tunanin kallonta da tabaron hangen nesa – don tana iya lalata maka idanu, har ta haifar da makanta.

Mafi kyawun abin da ke wanzuwa a gari

Bright red and orange clouds, over some dark mountains
Bayanan hoto, A wasu ɓangarorin na duniya, fitowa da faduwar rana na da ban sha’awa a baya-bayan nan

Kyakkyawan yanayin abin da kake hangowa a sama na sanyawa ka/ki rasa ta cewa, amma a nan akwai muhimman al’amuran biyu a gareka/ki: warwatsuwar dishi-dishin haske (‘Rayleigh’)

A haƙura da balgacewar alamun, sai dai ɗaukacin al’amarin abu ne mai kyau a tsohuwar ta’adar kimiyyar Fiziya (lissafin kimiyyar kai-kawon al’amura) da daɗaɗɗun siffofin hasken rana da ke ratsa sararin duniya,” a cewar masanin taurari Edward Bloomer na cibiyar nazarin sararin samaniya ta Royal Museum Greenwich.

Tashin farko dai muna bukatar fahimtar fasalin haske, wanda ya kunshi launukan hasken ziryan da ke bayyana- ja da rawaya da dorawa da shudi da toka-toka da ruwan goro.

Cigaban Labari…

Karin Wasu

Sababbin Wallafa