Connect with us

Fasaha

Dangantaka da bambanci tsakanin Kyamara da Idon dan Adam

Published

on

kyamara-da-idon-dan-adam

Dangantaka da bambanci tsakanin Kyamara da Idon dan Adam

Rubutun wannan makala ya samo asali ne duba da yadda dalibai suka bukaci a yi musu bayani cikin harshen Hausa akan wannan batu. Idan muka duba abubuwan guda biyun wato idon dan Adam da kuma kyamara zamu ga cewa lallai suna da alaaka musamman ta fuskar yadda suke gudanar da aikin su.

Shekaru da yawa da suka shude, masana sunyi bincike mai zurfi wanda har suka gano sirrin yadda idanuwan dan Adam ke aiki, wajan sarrafa hoto har su aika dashi cikin masarrafa wadda Allah ya halicci dan Adam da ita domin gani da kuma samun damar fahimtar duk abinda aka iya gani da idon. Ta hanyar Kimiyya da Fasaha aka gano har aka kai ga tsarawa da kirkirar wannan na’ura ta Kyamara (Camera), wadda kawo yanzu an samar da nau’i-nau’i na wannan na’ura manya da kanana, na sirri da na sarari gasunan birjik ana ta amfani da su har a wayoyin zamani.

Saboda haka a cikin wannan makaala zanyi gwargwadon bayani akan dangantakar su da kuma bambancin dake tsakanin su, domin asami kyakkyawar fahimta.

Kyamara da Idon dan Adam suna amfani da ka’idodi guda 3 wajan kamawa ko daukar hoto. Ita kyamara tana amfani da abubuwa kamar haka; shutter da aperture, da gilasai (lens) da kuma mafi muhimmanci wajan karbar haske da sarrafa hotuna wato fim wanda kyamarar da (analogue) ke amfani dashi ko kuma CCD ko CMOS sensors a kyamarar zamani (Digital)

Ga bayanin wasu kalmomi da nayi amfani da su a sama domin samun cikakkiyar fahimta a garesu;

SHUTTER da APERTURE: Su ne sassan dake da ruwa da tsaki wajan sarrafa hasken dake shiga cikin gilashin kyamara yayin daukar hoto. Kuma suna da matsanancin sauri wajan buduwa da rufewa kamar kiftawar ido.

FILM: Shi ne wanda ake amfani dashi a tsarin kyamara irin ta da ko ince na farko.Kuma a jikinsa hoto ya bayyana, wato shike adana hotunan da aka dauka.

CCD ko CMOS SENSORS: Su kuma wadannan sassa za’a iya samun daya daga cikin su a kyamarar zamani (Digital Camera). Kuma sune fasahar da ta maye gurbin tsari ko daukar hoto irin na kyamara analogue, sannan ana iya daukar hoto mai motsi (moving) ko maras motsi (still).

Bisa la’akari da wadancan abubuwa ne yasa kyamara tayi kamanceceniya da idon dan Adam wajan gudanarwa da sarrafawa domin samar da hoto ko hotuna.

kyamara-da-idon-dan-adam

Ga bayanin yadda idon dan Adam ke sarrafa sassan sa domin samar da gani ga dan Adam;

Sarrafawa da kaiyade adadin hasken dake shiga cikin idon dan Adam da kuma Kyamara

Kaiyade adadin haske

Sashen dake tsukewa ko kara fadi (Irish) na mashigar haske (pupil) a cikin idon dan Adam suke sarrafawa da kaiyade hasken dake shiga cikin ido kamar yadda shutter da aperture ke sarrfa haske a kyamara.

Daidaitawa da tattara Haske

Gilashin cikin ido da cornea suna aiki kamar yadda gilashin kyamara yake aiki wajan karkata hasken dake shiga cikin ido domin daidaita shi akan sashen dake sarrafa hoto (Retina) dake cikin ido ko fim da CCD a cikin kyamara.

Daukar Hoto

Mafi muhimmanci wajan dauka da sarrafa hoto  acikin idon dan Adam shi ne Retina kamar yadda CCD/CMOS yake a cikin na’urara Kyamara. Akwai kananan abubuwa guda biyu wadanda suke ginshikai wajan karba da tsara launika (colours) a sashen sarrafa hoto a cikin idon dan Adam wadanda aka kira Cones da Rods. Haka zalika, CCD/CMOS a cikin kyamara sune ke da alhakin karbar launika kamar yadda cones yake a cikin idon dan Adam. Kamar yadda aka tsara rods domin karba da sarrafa haske da inuwa a hoto mai launin fari da baki.

A bayyana yake karara, inda wadanan abubuwa guda biyu sukayi kama da juna shi ne, sashen dauka da sarrafa hoto na idon dan Adam (retina) da kuma sashe makamnacinsa a kyamara (sensor ko CCD ko CMOS) kaurin su daya (diameter) 35mm. Siffa ko fasalin masarrafar hoton idon dan Adam (Retina) a kumbure yake (curved), haka zalika ta masarrafar hoto a kyamara a mike yake (flat) hakan ya sa ake samun bambanci wajan ingancin hoto a massarafa hoto a cikin idon dan Adam.

A takaice, masarrafar hoto ta cikin idon dan Adam (retina) tana da karfin sarrafa hoto darajar inganci kimanin miliyan 576 sau miliyan (576 million megapixels) idan aka danganta shi da sabon samfurin kyamara kirar kamfanin Canon dake da darajar inganci 250 (250 megapixels). Wannan ya nuna karara irin tazarar dake tsakanin Kyamara da idon dan Adam.

Akwai tarin bayanai masu yawa wanda tsananin bincike ne zai bayyana su.

Duniyar Fasaha Online.

Continue Reading