Connect with us

Darasi

Shafukan intanet guda 11 da suka fi shahara

Published

on

shafukan -intanet

Darasi na 2 akan Shafukan intanet guda 11 da suka fi shahara

A cikin darasin farko nayi bayana akan me ake nufi da shafin intanet da sauran abubuwa masu fa’ida dangane da hakan, wanda yanzu zan dora da bayani akan ire-iren shafukan da suke a intanet da kuma irin bayanan da kowannen su ya kunsa.

Bincike ya bayyana cewa a kullum ta Allah ana kirkirar ko bude sababbin shafukan intanet (new websites) a kalla guda 380 a kowanne minti daya, wato kimanin shafuka guda 6 kenan a kowacce dakika guda.

Akwai shafukan intanet iri-iri, kuma kowanne yanada manufar sa, da kuma irin abubuwan da ake wallafawa a cikinsa, domin samun amfani a fadin duniya baki daya. Wadannan bambance-bambancen dake tsakanin su nake so na bayyana a wannan darasi domin a sami kyakkyawar fahimta akan kowannen su. Kasancewar suna da yawan gaske, zan mayar da hankali akan wadanda suka fi shahara a duniya, kuma wadanda akafi mu’amala da su a kowanne lokaci.

Shafukan intanet guda 11 da suka fi shahara

 1. Blog: Shafin intanet ne da yake bukatar sabuntawa akai-akai (regular updates). Zai iya kasancewa mallakin mutum daya ko mutane wajan bashi kulawa da wallafa sababbin al’amura. Kusan Shafukan Blog sun mamaye kaso mai girma a intanet. Ana iya tsara shafin blog akan kowanne irin al’amari domin yadawa a duniya baki daya. Bayani akan fitattun manhajoji 10 da ake tsara shafukan Blog
 2. Business Website: Shi kuma wannan shafin na kasuwanci ne, kuma shine ya maye gurbin shaguna ko kasuwannin mu na zahiri a intanet, tamkar duniya a tafukan hannun mu. Shine hanya nafi sauki wajan bayyana wa duniya irin abubuwan da mutum yake siyarwa, hanya ce ta jan hankalin abokan huldar daga sassan duniya baki daya. Ana sanya cikakken adreshi, cikakken bayani akan sana’a ko kasuwanci komai kankantar sa a idon duniya da sauran su… Kuma shi ma ana sabunta shi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
 3. Brochure Website: Shi ma wannan nau’in shafin intanet ne daya kunshi bayanan kasuwanci, musamman na kananan ‘yan kasuwa. Bayanan cikin sa takaitattu ne, wadanda basu gaza adreshi ba, da kuma jerin sunaye da hotunan kayayyaki, sannan kuma ba a sabunta shi kamar wadanda na bayyana a sama. Shi yana daga cikin rukunnan shafukan intanet masu lakabin STATIC WEBSITE. Kuma darajarsa bata kai na Business website ba.
 4. Crowdfunding Website: Shi kuma wannan sabuwar hanya ce ta zamani da ake amfani da ita wajan neman kudi ko jari daga jama’a masu ziyarar shafuka. Mutane masu fikira da basira musamman wadan da basu da gata sukanyi amfani da wannan shafuka wajan neman tallafi daga duniya. Haka yana basu damar cigaba da yin abubuwanda mutane ke da bukatar samu a shafukan su. Misalin shafuka irin wannan akwai  Kickstarter da Crowdcube
 5. Ecommerce Website: Shi kuma wannan shafin intanet ne da ake saye da siyarwa kai tsaye a cikin sa. Wannan nau’i na shafin intanet ya sha bamban da na business website. Shi wannan ana siya ko zabar abubuwan da ake bukata, sannan a biya kudin su kai tsaye ta wannan shafi. Misali Jumia, Konga, Aliexpress da sauran su…
 6. Educational Website: Wannan kuma shafi ne da ya kunshi al’amuran koyarwa. Manyan cibiyoyin ilimi na duniya suna amfani da shafukan intanet wajan ilimantar da daliban su. Haka zalika jama’a masu kishin al’umar su, suna bude shafuka domin yda ilimi ta hanyoyi da yawa kama daga Wallafa litattafai, Littafi cikin sauti, da kuma fayafayen bidiyo wadanda ake bayyana aiyukan ilimi a aikace domin samun kykyawar fahimta a tsakanin amsu ziyarar shafukan ko mabiyan su. Misali Coursera da EdX Da sauran su…
 7. Media ko Entertainment Websites: Su kuma wadannan shafuka ne da a kullum ake sabunta su, kuma ana wallafa abubuwan da suka shafi labarai da al’amuran yau da kullum kamar su; wasanni, nishadi da kuma hasashen yanayi da sauran su… misali CNN da Hollywood. Kamar yadda na bayyana ire-iren wadannan shafuka suna bukatar sabuntawa akai-akai.
 8. Nonprofit Website: Shi kuma wannan shafin ne na kungiyoyi ma su zama kan su, wadanda ake budewa domin neman tallafin (donations) kudi, kayan sawa da sauran abubuwan bukata domin tallafawa mutane gajiyayyu, marasa karfi ko gata, ko wadanda annoba ta fakawa, ko rashin lafiyar dake bukatar manyan kudi wajan kulawa da sauran su… Shafuka ne da ake budewa ba domin kasuwanci ba. kuma suma akwai bukatar sabunta abubuwan da ke cikin sa akai-akai domin nunwa duniya ire-iren aiyukan da sukeyi. Ana iya basu kyautar kudi ko taimako daga sassan duniya. Misali The Kwandala Foundation da sauran su…
 9. Personal website: Wannan kuma shafi ne na qashin kai wato mallakar wani mutum domin wallafawa da yada tunanin sa, Hutuna, bayyana aiyukan sa, tarihin rayuwar sa, bayyana matakin ilimi da na kwarewa akan aiyuka (CV) da sauran al’amura. Kuma yanada saukin kirkira. Bayani akan yadda mutum zai bude personal website
 10. Portal Website: Shi kuma wannan shafi ne mallakin cibiyar Ilimi ko Ma’aikata ko Na kasuwanci. Kuma akan tattara dukkan muhimman al’amuran da suka shafi Dalibai ko ma’aikata kama daga labarai, horaswa ta fannin ilimi, ko yada sababbin al’amura, ko sarrafa sashen sakonni na email da sauran su… wanda akwai bukatar kowa ya mallakai bayanan sirri (login access) domin samun damar mu’amala shafin. Akwai misalin Portal website wato shafin Yahoo wanda ya kasance matattarar muhimman al’amura daban-daban a cikinsa.
 11. Portfolio Website: Shi kuma wannan ya dara personal wensite domin zai iya zama shafin marubucin litattafai, Mai zane-zane, ko na ma’aikata masu zaman kan su (Freelancers) da sauran su… Ana bayyana dukkan aiyuka cikin hotuna, basira, fikira da baiwa wajan gudanar da aiyuka a shafin.

Dafatan Allah ya amfanar damu baki daya.

Dan Allah a dinga yin comment

 

Continue Reading