Connect with us

Darasi

Fitattun manhajoji ko hanyoyi 10 da ake tsara shafin Blog

Published

on

Fitattun manhajoji ko hanyoyi 10 da ake tsara shafukan Blog

Darasi na 3: Fitattun manhajoji ko hanyoyi 10 da ake tsara shafin Blog.

Aikin rubuce-rubuce tsohuwar sana’a ce a duniya. Tun daga rubutun litattafan addini, tarihi, fannonin ilimi, tatsuniyoyi, labarai na al’amura daban-daban da sauran su… Haka zalika kowanne marubuci yana bukatar abubuwa ko kayan aiki, kama daga alkalami, takarda ko fata, launika domin tsarawa da inganta rubutu sannan uwa uba yana bukatar nutsuwa, nazari, da tunani mai zurfi jan hakula da fahimtar da mai karatu. A kowanne zamani akan sami cigaba ta fuskoki daban-daban wanda shi ne ya kawo mu zamani shafukan intanet da muke amfani da su a fadin duniya baki daya.

Zuwan intanet ya kawo sauye sauye a rayuwa da kuma yadda ake gudanar da aikace-aikace a fannoni daban-daban. Ta kai ta kawo kusan dukkan al’amura sun koma intanet. A taikace marubuta suma sunyi kaura zuwa shafukan intanet domin su ma adama da su. Zan iya cewa intanet gidan marubuta ne. Su suke raya dukkan al’amuran intanet. hakan ya kawo mu gabar da zan bayyana hanyoyi ko manhajoji guda 10 da marubuta zasu iya amfani da su wajan wallafa komai a intanet. Musamman tsarin wallafar da aka yiwa lakabi da Blogging.

Ana iya bude shafin blog akan abubuwa masu yawan gaske amma ga kadan daga cikin su; koyar da dabarun kasuwanci ko sana’o’i, koyarda karatu, dabarun aiwatar da wasu aikace aiakce musamman ta hanyar fasaha, koyar da girke-girke, koyar da dinki na zamani da sauran abubuwan da bazan iya tunawa ba a halin yanzu. Shafukan blog suna bukatar lokaci da kuma dagewa wajan zakulo darussa masu ma’ana wadanda zasu ja hankulan masu karatu. Shafin blog yana bukatar sabunta rubutu ko abubuwan da ake tattaunawa akansu domin samun maziyarta a kowanne lokaci, wanda haka ka iya zama dalilin samun kudi ta shafin blog.

Manhajojin da ake amfani da su wajan wallafa shafukan blog suna da yawa, kuma akwai na kyauta da kuma na kudi. Sannan kuma suna kunshe da dukkan abubuwanda marubuci ke bukata a kowanne lokaci domin kawatwa da inganta aiyukan sa. Akwai tsarin dorawa ko saka hotuna, sauti har da fayafayen bidiyo duk a cikin tsarin shafukan blog. Iya fahimta mutum, iya abubuwan da zai iya aiwatarwa a tsarin rubutu a intanet. Na dan tsakuro hanyoyi ko manhajoji guda 10 na kyauta da za a iya amfani da su wajan tsara shafukan blog, kamar haka;

  1. WordPress – Wannan manhajar ta wordpress tana da tsari mai kyau da saukin sarrafawa a wajan tsara blog da sauran shafukan intanet. Kusan kaso 80 cikin dari na shafukan intanet dukkan su na wordpress ne. Kuma Tana da tsaro sosai. tana samun sabuntawa akai-akai. kuma ana samun manhajar a wordpress.org.
  2. Wix – Shi kuma wannan shafi ne na musamman da suke ba da damar kera shafukan intanet kowanne iri a kyauta, kuma suna da tsarin blog.
  3. Squarespace – Shi ma wannan yanada tsari na zamani wajan cakuda rubutu da hotuna a shafin blog.
  4. Weebly – Shi ma wannan shafi ne da suke bada damar bude shafukan blog cikin sauri da sauki. Har ikirari sukayi cewa sune na 1 wajan iya kira da kuma wadatar kayan aikin shafin blog a intanet.
  5. WordPress.com – Wannan shi ne mafi girma da kuma shahara wajan bada damar bude shafukan blog. Akwai alaaka tsakanin wordpress.com da kuma wordpress.org. Bambancin dake tsakanin su shine; wordpress.org suna bada damar sauke manhajar su, ko yin amfani da manhajojin su a wasu shafuka masu zaman kansu, su kuma wordpress.com sai dai ka bude blog akan shafin su kawai.
  6. Blogger – Kusan wannan shi ne na farko daga cikin jerin hanyoyin bude shafin blog a intanet. Amma yanada iyaka dangane da abubuwan da za a iya aiwatarwa, sannan yana bukatar fahimta sosai wajan aiki da shi. Kuma ya kasance mallakin kamfanin Google ne. Yanada tsari mai kyau sosai, musamman idan aka fahimci lungu da sako na yadda za a tsara shi.
  7. Tumblr – Wannan ma yanada kyau sosai da saukin aiki wajan tsara blog. Yanada kyau wajan wallafa takaitattun bayanai ko hotuna.
  8. Strikingly – Shima wannan yanada tsari mai kyau da sauki wajan wallafa shafukan intanet. Yanada tsari irin na shafi mai bango daya (One page), wanda kusan shine tsarin da akafi aiki da shi a wasu bangarori na intanet.
  9. SITE123 – Wannan shafi suna da tsari na musamman wajan taimakawa mutane masu sha’war bude shafukan blog. Suna nuna faifan bidiyo akan yadda mutumzai bude blog.
  10. GoDaddy – Wannan zan iya cewa sabo ne. Amma suna da tsarin taimako wajan bude shafin blog da sauran su… Amma yanda kyau suma a jarraba su.

Kowanne za a iya amfani da shi wajan bude shafin blog. Za ku iya ziyartar kowanne domin ganin yadda tsarin su ya ke.

Da fatan Allah ya amfanar damu.

Continue Reading