Connect with us

Darasi

Darasin Kwamfuta na 2 – Hardware

Published

on

Na'urar Kwamfuta

Darasin Kwamfuta na biyu (2) – Hardware

A cigaba da darasin Kwamfuta, a cikin kashi na biyu zan fara da bayani akan daya daga cikin jigajigan sassan Kwamfuta wato Hardware. Kamar yadda zamu gani cikin hoton dake kasa da wannan bayani.

sassan kwamfuta

Sassan Kwamfuta

Kamar yadda muke gani a cikin hoto akwai sassa da aka rubuta sunayen su kamar; CPU, Monitor, Keyboard da kuma Mouse. Wadannan sassan kwamfuta da muke gani sune abubuwan da ake bukata a matakin farko a matsayin cikakkiyar kwamfuta wadda za ayi aiyuka da ita.

Su wadannan sassa wadanda muke iya gani, muke iya tabawa an kasa su rukunni mabambanta daidai da tsarin gudanar da aiyukan su kamar haka;

Input Devices: Sassan da ake aikawa da umarni zuwa ga masarrafi (CPU) dake cikin akwatin computer domin sarrafawa. Misalan su; Keyboard, Mouse, Microphone, scanner, Joystick da sauran su…

sassan-shigar-da-aiki

Sassan shigar da aiki

Processing Devices: Wadannan sassan kwamfuta ne da suke da ruwa da tsaki wajan sarrafa duk aiyukan da akeyi da kwamfuta. Misalan su; Motherboard, Random Access Memory da kuma CPU.

sassan-sarrafa-aiki

Sassan sarrafa aiki

Output Devices: Su kuma sune sassan kwamfuta da suke fitarwa ko nuna sakamakon aiki a matakin karshe bayan sarrafawa. Misalan su; Monitor, Speaker, Printer da sauran su…

sassa-masu-fitar-da-sakamako

Sassan bada sakamakon aiki

Communication Devices: Wadannan sassa sune kanwa uwar gami wajan sadarwa tsakanin na’urori. Misalan su; Modem, NIC da sauran su.

sassan-sadarwa

Sassan Sadarwa

Storage Devices: Suma wadannan sassa suna da matukar muhimmanci ga na’urar kwamfuta wadanda suke a matsayin rumbu ko wajan adana dukkan aiyukan da aka sarrafa. Misalan su; Hard disk drive (HDD), RAM, ROM da sauran su…

sassan-adana-aiki

Sassan adana aiki

Sannan kuma bayan wadannan sassa akwai wasu da akayiwa lakabi da Pheripheral Devices. Sun kasance dukkanin sassan da rashin su bazai hana kwamfuta aiki ba, amma suna da muhimmanci a gare ta. Misalan su; keyboard, mouse, printer, Camera da sauran su. Suna taimakawa kwarai wajan sarrafa na’uarar kwamfuta da danginta.

Cigaban karatu na nan tafe….

Continue Reading