Connect with us

Darasi

Darasin Kwamfuta na uku (3) Software.

Published

on

Manhajar-sarrafa-naura

Darasin Kwamfuta na 3 – Software.

A cigaban darasin Kwamfuta na wannan shafi, yau zan yi bayani ne akan Manhaja wato Software da rassansa guda uku.

Yanada kyau ayiwa software kyakkyawar fahimta kwarai da gaske a matsayin sa na tsararrun umarni da ke sarrafa dukkannin sauran sassan na’urar kwamfuta wato Hardware da kuma sauran al’amura dake tafiyar da aiyukan na’urori.

Softawre ya kasu rassa uku; (1) System Software da kuma (2) Application Software da kuma (3) Utilities Software. Wadannan rassa guda biyu daga cikin ukun sun zamo tilas ga na’urar kwamfuta da dange-dangenta, domin samun damar gudanar da aiyuka dasu.

(1) SYSTEM SOFTWARE (Manhajar Sarrafa Na’ura) shine na farko da ake sakawa (Install) na’ura domin a sami kyakkyawar fahimtar gudanar da aiyuka tsakanin sassan na’ura da muke gani, da tabawa lokacin gudanar da aiki (Hardware) da kuma wadda (User ko Operator) ke sarrafa ita na’uarar. Wannan manhaja itace akafi fahimta da OPERATING SYSTEM. Kuma akwai nau’i-nau’i na wannan manhaja kamar su;

  • Microsoft Windows. Wanda sune suka fi shuhura a duniya tun shekarar 1985, suka kawo gagarumin sauyi wajan sarrafa Kwamfuta. Kuma haryanzu ana ta fafatawa da wannan manhajar sarrafawa ta Windows. A halin yanzu Windows 10 shine sabo wanda ludayinsa ke kan dawo.
  • Apple iOS. Shima wannan yayi shuhura sosai kuma kamfanin Apple ne ya samar da shi. Kuma yana aiki ne akan wayoyin su samfurin iPhone da iPad da iPods da sauran su. Haka kuma yana da tsaro akan yadda masu amfani da na’urorin kamfanin apple sune sahihai wajan manhajojin su.
  • Google’s Android OS. Shima wannan yayi shuhura sosai kamar yadda kai mai karatu ka sani cewa ana amfani da wayoyi samfurin Android fiye da sauran wayoyi. Duba da saukin su wajan mallaka. Kuma Kamfanoni da yawa suna amfani da wannan manhaja ta Android, ba kamar na kamfanin Apple ba da sai wayoyin su kadai za suyi amfani da manhajar sarrafawar su. Wayoyi samfurin android sun zama ruwan dare a kowanne mataki.
  • Apple macOS. Kamar yadda manhajar Apple iOS yake ga wayoyi samfurin iPhone da sauran su… Shima haka yake akn Kwamfutoci samfurin Apple wanda suka hada da Laptop da kuma ta girke (Desktop). Kamfutoci da wayoyi samfurin Apple sunyi shuhura wajan matsanancin sauri, babban rumbu da kuma tsaro fiye da sauran na’urori masu amfani da wasu manhajojin sarrafawa da ba na Apple ba.
  • Linux Operating System. Shi kuma wannan ya sah bamban da sauran da na bayyana a sama. Saboda babu Kamfani takamaimai da zai bugi kirjin cewa shi ya samar da shi. Linus Torvalds shine kwararren da ya samar da shi a shekarar 1991. Kuma masana gwanaye wajan iya kirar manhaja sukayi tarayya wajan tallafawa da kuma daga darajar ta kowanne tsari a matsayin manhaja (Open source). Kuma an samar da manhajojin sarrafa na’urori a karkashin wannan manhaja masu yawa, kamar su Ubuntu, Kubuntu da sauran su…. hasali ma anyi amfani da wani sashe na linux a manhajar Android. A halin yanzu manyan kamfanoni da manyan cibiyoyin bincike suna amfani da wannan manhaja.

Cigaban karatu na tafe….