Connect with us

Fasaha

Fasaha ce hanyar magance yaduwar coronavirus

Published

on

gudanar da aiki daga gida domin magance yaduwar cutar corona virus

Fasaha ce hanyar magance yaduwar coronavirus

Nasan mai karatu zaiyi mamakin wannan furucin ‘Fasaha ce hanyar magance yaduwar coronavirus”. To amma ba abin mamaki bane duba da yadda al’amuran duniya suke sauyawa a kowanne lokaci ta hanyar amfani da kimiyya da fasaha.

Kusan a halin yanzu babu wani abu da ake tattaunawa kansa duniya baki daya da ya wuce cutar Coronavirus. Saboda cutace mai yaduwa ta hanyoyi da dama, wadda saboda irin illolin dake tattare da ita, kasancewar kafafen sadarwa musamman masu yada labarai har kullum su na bayyana irin ta’adin da wannan cuta take yi kasashen da suka kamu da ita.

Takai ta kawo a wasu kasashen an hana cudanya ga jama’a domin dakile yaduwar ta a tsakanin a’umma. Kuma a halin yanzu ana ta kokarin shawo kanta a duniya baki daya. Bazan cika ku da surutu akan irin illar wannan cuta ba saboda labarinta ya zamo ruwan dare. Zan mayar da hankali ne akan yadda ake amfani da fasaha domin gudanar da al’amuran rayuwa na yau da kullum ba tare da anyi cudanya ba a tsakanin jama’a wanda hakan shi ne matakin da kasashen duniya suka dauka a matsayin kariya musamman kasashen da akafi samun masu cutar.

Tuntuni fasaha ta samar da tsarin gudanar da aikin ofis daga gida (Work from home), ko karatu daga gida (Remote Learning har ma da siye da siyarwa daga gida ta shafin intanet. Haka zalika a halin yanzu wannan al’amari ya kara samun karbuwa, duba da yadda cudanya ko mu’amala ta zahiri tsakanin al’umma ya zamo barazana ga lafiyar su a duniya musamman a kashen da cutar ta fi yin illa.

Labarai sun bayyana cewa kasar Sa’udiya ma ta dauki matakin rufe manya da kananan makarantu, domin dakile yaduwar wannan cita a tsakanin. Haka ma kasashe da yawa sun dauki wannan tsari na rage cudanya tsakanin al’uamma domin asamr da kariya. To abin dubawa anan shine; Matakan tsaro ga na’urori da sadarwa tsakanin na’urorin domin haki da cutar na’urar kanta har ma da masu kutse.

Saboda kada ya zamo ana maganin kaba kuma kai yana kumbura. Wato kada ya zamo ana maganin yaduwar cutar coronavirus a tsakanin al’aumma, ba tare da an dauki kwararan matakan kariya ga na’urori da sadarwar su dangane da ta su cutar Virus da masu kutse ba. Dole ne a samar da matakan tsaro wajan yin karatu, aiki da sauran al’amura da ake iya gudanarwa ta hanayar fasahar sadarwa ta intanet.

Fasahar tsaro ta VPN a tsarin sadarwa tsakanin na’urori da intanet

mataki tsaro na VPN

Wannan dalili ya sanya aka kirkiro da tsarin amfani matakin tsaro ta sadarwa tsakanin na’urori da intanet (VPN). Wanda a halin yanzu shi ne tsarin da wadancan kasa she da suke amfani da fasaha wajan gudanar da aikace-aikacen yau da kullum. Saidai wani hanzari ba gudu ba, wannan hanya ko fasaha ta VPN tana da muhimmanci, kuma yanda kayu a fahimci yadda take, kamar haka;

  • Tana rage saurin intanet saboda yawan killace-killace dake cikin tsarin ta
  • Samarda wannan fasahar ta VPN ta kashin kai akwai tsadar gaske.
  • Kuma yana da kyau a sani cewa VPN ba intanet ba ne. Amma da matakin tsaro ne na sadarwa tsakanin na’urori da intanet.
  • Tana da saukin aiwatarwa ga kowa
  • Idan har ana amfani da intanet irin na kyauta kamar (Pulic Wi fi), ya zamo dole ayi amfani da VPN domin tsaro.

Insha Allahu zanyi cikakken rubutu nan gaba akan VPN domin a sami fahimtar tsarin sosai.