Connect with us

Fasaha

Fasaha: Illolin amfani da Manhajar VPN

Published

on

illolin amfani da manhajar vpn

Tun bayan dakatarwar da Gwamnatin Tarayyar Najeriya tayi wa shafin Twitter, wasu ‘yan kasar suka rungumi tsarin amfani da wata manhaja ta zillewa hanin da ake kira VPN domin ci gaba da amfani da shafin na twitter.

Manhajar VP na sada na’urar mai amfani da ita da shafukan da aka toshe

Manhajar na aiki ne wajan haɗa wayar mutum da sadarwarsa ta Internet ba tare da wata barazana ba, sannan idan ka hada manhajar da Internet dinka, wannan zai ba ka cikakkiyar kariya wajan ziyartar shafukan da watakila aka dakatar ko aka toshe.

Akwai manyan nau’ikan manhajar ta VPN guda biyu, waɗanda ake iya amfani da su a kyauta da galibin su ‘yan Najeriya suka fi amfani da su, da kuma waɗanda sai an biya kuɗi.

Amfani da manhajar VPN ta kyauta na iya jefa ka cikin haɗari, za ta iya janyo maka abinda ko da wasa baka taɓa tunani ba, gara ma wadanda ake biya kafin amfani da su domin sukan iya kare bayanan mai amfani da su a kan kudin da bai taka kara ya karya ba.

Idan kuwa ra’ayinka shine amfani da manhajar VPN na kyauta ne, to ya kamata tun wuri ka san irin kalubalen da ke tattare da hakan, gasu a ƙasa za mu yi bayani daki dai.

Za a iya satar bayananka wajan amfani da VPN na kyauta

Yawancin masu amfani da VPN basu da masaniyar za a iya satar bayanansu cikin sauƙi

Ɗaya daga cikin muhimman dalilan amfani da manhajar VPN shine ganin an kare ka daga masu kutse, to amma fargabar ita ce maganar gaskiya wasu manhajojin na VPN na kunshe da wani siddabaru da ake amfani da shi wajan satar bayananka da kuma amfani da wannan dama wajan aiwatar da wata mummunar manufa da ake son cimmawa.

Irin waɗannan manhajoji na kyauta na VPN na amfani da tallukan da suke sanyawa masu amfani da su wajan wawashe bayansu, kasancewar sun dogara ne da ‘yan tallukan da suke samu wajen samun kudin shiga.

Bibiyar dukkan ayyukan masu amfani da VPN

Babban dalilin da ya sa mutane ke amfani da VPN bai wuce kare sirrinsu a lokacin da suke bincike a Internet ba, to sai dai yawancin manhajojin VPN na kyauta na da wasu mutane da aka sanya da ke bibiyar abubuwan da ke faruwa a cikinsu, suna tattara bayanan masu amfani da su, don haka a wannan bigire maimakon a aiko maka da wani tsari da kake da damar amincewa da shi ko ka latsa kalmar a’a, sai kawai a tunkudo maka talla, wanda a lokacin da kake kallonsa sai kuma a rika kwasar bayananka salin alin ba tare da ka danna komai ba.

Iyakance Samun Bayanai

Yawancin VPN na kyauta na iyakance adadin bayanan da za ka iya amfani da su. Suna yin wannan ne don tura masu amfani da su zuwa tsarin da ake biyan kuɗi kafin a samu cikakkiyar damar yin abinda ake son a yi, kamar yadda Hausawa ke cewa ”Iya kudinka iya shagalinka”

Manhajar VPN na haifar da damuwa ga masu amfani da ita saboda yadda take jinkirta sadarwar Internet (rashin sauri).

Manhajar VPN ta kyauta na haifar da jinkiri wajen samun bayanai a Internet, abun da ke kawo damuwa ga wanda ke amfani da su, to dalilin shine yawancin mutane na raja’a ne ga na kyauta don cin bulus.

Sannan su kansu tallukan da suke sanyawa da zummar satar bayanai na iya haifar da rashin saurin na Internet, dalilin sanya tallan shine tunda masu amfani da su garabasa kawai suke ci, to bari su tallata wata haja tunda dama masu karin magana sun ce ”Da ruwan ciki akan ja na rijiya”.

Barazanar harbuwa da cutukan intanet

Manhajojin da ake amfani da su wajan sada waya ko na’urar kwamfuta da Internet na ɗauke da wasu hanyoyi da yawa da ake sanyawa a cikinsu wajan satar bayanai ko yin kutse ko shirya wata kutungwila.

Wasu manhajojin na VPN da ake amfani da su a kyauta ana tsara su ne da zummar cewa masu su na da ikon sarrafa bayanan mutane yadda suka ga dama, kuma suna ba da wannan ikon ga abokan cinikinsu masu biyan kuɗi don riba.

Wannan yana da matukar hadari kamar yadda masu aikata laifuka ta yanar gizo ke iya yin amfani da wannan yanayin don ƙaddamar da hare-hare kan masu amfani da VPN da basu da masaniyar duk wannan al’amari.

Manhajojin VPN na tattare da cukumurda iri iri da ke da bukatar zuba kudi da yawa a harkar don samar da kariya da kuma tsare bayanan masu amfani da su,

Akwai kuma buƙatar masu su, su riƙa sabunta tsare tsaren bada kariyar da suke amfani da su a kai a kai dai dai da zamani domin tabbatar da kare abokan huldarsu.

Sai dai kash, rashin mayar da hankali ga wadannan abubuwa da suka kamata ne ya sa masu manhajar VPN ta kyauta ke cin karensu ba babbaka ta hanyar cusa talluka da wasu tsare tsare da ke zama babban haɗari ga masu amfani da manhajar.

A ƙashin gaskiya, wannan ba wai kawai abu ne mai matuƙar haɗri ba, ya kuma ci karo da dokokin bayar da kariya da tsaro da su kansu ka’idojin amfani da manhajojin na VPN.

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku