Connect with us

Fasaha

Fasaha: Wata Matashiya Ta ƙirƙiri Manhaja Kan Fyaɗe a Jihar Kano

Published

on

kano lady sa'adatu aliyu

Wata matashiya a jihar Kano a arewacin Najeriya ta ƙera manhajar da za ta dinga bayar da rahotanni kan fyaɗe. Wannan batu ya ja hankalin ƴan Najeriya a kafofin sada zumuna musamman Twitter.

Saadat Aliyu ƴar asalin jihar Kano ta samar da sabuwar manhaja ce ‘Helpio’ mai bayar da bayanai kan cin zarafin mata wacce ta ƙaddamar a rumbun manhaja na wayoyin android wato Play Store a shekarar 2020.

Saadat ita ce shugabar kamfanin Shamrock Innovation mai ƙirƙire-ƙirƙiren fasaha kuma mai fafutikar ci gaban mata a fannin ƙirƙira.

Yadda aka gabatar da matashiyar a kanun labaran wasu jaridun ƙasar a matsayin ‘Kano Lady’ wato budurwa ƴar Kano shi ya ja hankalin ƴan Najeriya a kafofin sada zumunta musamman a Twitter.

“Kano Lady” na cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a shafin Twitter tun daga ranar Litinin zuwa Talata inda kusan mutum 15,000 suka yi tsokaci akai.

Trending

Duk da ba kasafai akan samu mata ba a fagen ƙirƙirar fasaha a Najeriya musamman arewacin ƙasar ba, amma wasu na ganin ta cancanci yabo kuma ya dace a kira ta da sunanta na yanka.

Yawanci dai kafafen yaɗa labarai kan alaƙanta mutum da sunan garinsa musamman wanda ba sananne ba.

Me ake cewa?

Abin da yawanci mutane suka fi tattaunawa shi ne rashin kiran matashiyar da sunanta na asali.

Suna ganin irin fasahar da ta samar bai dace a mayar da hankali ga garin da ta fito ba.

@bheyeh_ ta ce: Ai Kano Lady tana da suna ko? ya kamata a ambaci sunanta don mu jinjina mata.

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

@Mbahdeyforyou ya ce: Idan da laifi ta aikata da an ambaci sunanta.

@Fawwarz ya ce: Maimakon sunanta, yanzo ga shi Kano Lady ya zama batun da aka fi tattaunawa.

@Pharm_ada tambaya ta yi cewa: Ko me ya samu sunanta… Menene kuma Kano Lady

Kauce wa Twitter, 2

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 2

Dalilin ‘Kano Lady’ ne ya sa sunanta na asali Saadat Aliyu ya kasance cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a Najeriya a Twitter a ranar Talata.

@Mayorspeaks ya ce: “Saadat Aliyu ce ta samar da manhajar bayar da rahotanni kan fyaɗe, Kano Lady ba sunana ba ne.

Kauce wa Twitter, 3

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 3

Shi ma @TAYOCONGA ya ce: Tana da suna kuma sunanta Sa’adiyat Aliu. bai dace a kira ta da Kano Lady ba. Ta ƙirƙiri manhaja a android domin bayar da rahoto kan batun fyaɗe. Ta cancanci a yaba mata.

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku