Connect with us

Ga me da Ni

Engr. Kabir Saleh

Kabiru Saleh

Na kasance mai kishi da karambani wajan fassara al’amura da yawa, zuwa harshen Hausa. Musamman abinda ya shafi fannonin Kimiyya da Fasaha. Duba da Muhimmancin Ilimi ga rayuwa al’umma da kuma yadda wadannan fannoni na Ilimi suka kawo gagarumin sauyi a duniya baki daya.

Fahimtar wadannan fannoni da harshen Hausa zai kawo mana babban sauyi da kuma cigaba a wannan nahiyar (Arewacin Najeriya). Duba da yadda akayi mana nisa a wasu sassa na kasar mu. Da kuma yadda ake nazarin wadannan fannoni na ilimi a makarantu manya da kanana, cikin harshen Nasara (English) wanda ya kasance bakon harshe a gare mu. Hakan yasa ba kowa ne yake iya fahimtar su yadda ya kamata ba a wannan nahiyar tamu.

Sannan kuma ina gudanar da aikyukan bude shafukan internet ga masu bukatar kasancewa a tsari irin na zamani; Kama daga shafin Kasuwanci, shafin rubuce-rubuce (blog), shafin karatu, shafin maikatu, shafin sada zumunta da sauran su… Kuma ina aikin gyara dukkan shafin da yake da matsala domin inganta saurin budewar sa da kuma kara tsaurin matakan tsaron shafin. Kuma dukkanin aiyukan inayin su a farashi mai sauki.

Da wannan yunkuri nake neman agaji ga Iyayen mu, Malaman mu Masana kuma kwararru a wadannan fannoni da su tallafa mana wajan kara fahimtar da mu, da yi mana gyare-gayre a bisa kurakurai da za’a iya cin karo da su a wannan shafi.

Muna fatan Ubangiji Allah ya amfanar damu baki daya.

Kabiru Saleh.