Connect with us

Ga me da Shafin Duniyar Fasaha Online

Wannan shafi, an samar da shi da nufin inganta fahimtar al’amuran Fasaha da Kimiyya ga al’ummar Hausawa, musamman Dalibai masu nazari a wadannan fannoni da kuma sauran Jama’a masu ta’ammali da Na’urorin Zamani, Fasaha da sauran al’aumara masu alaka da wadannan.

Idan muka duba za muga cewa akwai kasashe masu yawa da suka shahara a fannoni daban daban, musamman kere-kere da kirkire-kirkire wadanda kullum sai karuwa sukeyi a fadin Duniya. Wadancan kasashe da yawan su suna amfani da harsunan kasashen su ba turanci ba. Hakan ya basu babbar nasara wajan samun kyakkyawar fahimtar ilimin kimiyya da fasahar da har takai su ga kasancewa a dukkan matsayin da suke kai a Duniya.

Wadannan dalilai sune sanadiyyar bude wannan shafi, duk dacewa ba shine na farko ba wajan bayyana kimiyya da fasaha cikin harshen hausa. Duniyar Fasaha Online ya samu damar kasancewa a cikin jerin gidajen radio na zamani wadanda ke gabatar da shirye-shiryen su a internet. A halin yanzu za a iya sauraron tashar DFOnline Radio a Radio Garden da kuma manhaja wadda zata saukaka mu’amala da wannan shafi da kuma samun sababbing al’amura a duk lokacin da aka wallafa su.

***Jan Hankali***

A tsarin fassara daga harshen turanci zuwa harshen hausa, ba a kowanne lokaci a ke samun kalmar hausa da zata maye gurbin kalmar turanci kai tsaye ba. Saboda haka a wannan shafi ana amfani da bayanai har da misalai masu gamsarwa da saukin fahimta ga masu karatu ko nazari a wannan fanni.