31 C
Kano
Thursday, October 22, 2020

Garba Shehu ya ta da ƙura a shafukan sada zumunta

Mafi Shahara

Kamar yadda ya saba, a yunƙurinsa na kare gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya kunna wutar muhawara tsakaninsa da ‘yan Najeriya game da farashin man fetur.

Ce-ce-ku-cen ya fara ne tun ƙarfe 10:00 na daren Talata jim kaɗan bayan mai magana da yawun shugaban na Najeriya ya wallafa wani shafin jaridar Punch da ke cewa ana sayar da litar man fetur kan naira 600 a shekarar 2013.

An fara amfani da maudu’in Garba Shehu a shafin tuwita inda a ranar Laraba shi ne na 13 cikin masu tashe a tuwita.

“Kar ku bari jam’iyyar PDP ta ruɗe ku. Yayin da ake cikin matsi, sun sayar da man fetur kan N600 a Lahadin Easter a 2013 (ku duba Punch ta ranar),” Garba Shehu ya wallafa a Tuwita da Facebook.

Kauce wa Facebook, 1

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 1

A shafin Facebook an mayar wa da Garba Shehu martani sau fiye da 4,000 aka kuma rarraba shi sau fiye da 1,500. Atuwita kuwa an mayar masa martani fiye da sau 2,300.

Martani

Kafin ka ce kwabo aka fara mayar masa da martani iri-iri ciki har da Oluwasegun Moses (@Oluwase23848602) wanda shi ma ya saka wani hoton kan labarin jaridar Punch ɗin sannan ya ce: “Ko ka san cewa an sayar da fetur kan N600 a Disamban 2017 da kuma Nuwamban 2019.”

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Shi ma Reuben Oshomagbe (@ReubenOshomagbe) ya ce: “Me ya sa ko da yaushe ‘yan siyasa ke tunanin tura zargi kan wasu shi ne maganin rashin ƙoƙarinsu a gwamnati.

”Garba Shehu na cikin gwamnatin da ta shekara biyar amma har yanzu yana ƙorafi kan abin da wata gwamnati ta yi a 2013.

Kauce wa Twitter, 2

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 2

An sayar da litar fetur kan N600 a 2019

Bincike ya nuna cewa ba a shekarar 2013 ba ne kawai (lokacin mulkin PDP) aka sayar da litar fetur ɗin kan N600, kamar yadda Garba Shehu ya yi ƙoƙarin nunawa.

Rahoton jaridar Punch na ranar Talata 12 ga watan Nuwamban 2019 ya ruwaito cewa ana sayar da litar man fetur kan N600 a garuruwan da ke kan iyakar Najeriya da wasu ƙasashe.

Mazauna garuruwan Sokoto da Katsina Ogun da Legas da Adamawa sun yi ƙorafin sayen litar man a kan N600 alhalin kafin wannan lokacin sukan saye shi kan N145.

Hakan ya biyo bayan umarnin da gwamnatin Buhari ta bayar na haramta sayar da man a duk gidan mai da yake garuruwan kan iyaka matuƙar bai wuce nisan kilomita 20 ba daga kan iyakar.

Kazalika, rahoton jaridar intanet ta Premium Times na ranar Litinin, 25 ga watan Disamban 2017 (ranar Kirsimeti) ya ruwaito sayar da man kan N600 a Abuja, babban birnin ƙasar.

Yayin da mazauna yankunan da ke wajen garin Abuja kamar Zuba da Gwagwalada suka sayi man kan N600, mazauna Kpegyi Junction kuma sun saye shi ne kan N350, kamar yadda jaridar ta gano.

Wannan layi ne

Ƙarin farashin mai a mulkin Buhari

Karin farashin mai na farko da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi shi ne ba da damar sayar da man a kan naira 87 da kobo 50 a gidan man ‘yan kasuwa ko da yake farashin bai sauya ba a gidajen man NNPC.

Tun daga wannan lokaci ba a sake samun ƙarin farashin man ba sai a ranar Laraba 11 ga watan Mayun 2016 da gwamnatin Shugaba Buhari ta mayar da shi naira 145.

A watan Maris 2020 – faɗuwar darajar fetur a kasuwar duniya ta sake tilastawa gwamnatin rage kudin man daga N145 zuwa N125.

Bayan wata guda, a karo na biyu a watan Mayun 2020, hukumar ƙayyade firashin albarkatun man fetur ta PPPRA ta sanar da sabon farashi daga N121.50 zuwa N123.50 lita guda.

Sai kuma a ranar Laraba 2 ga watan Satumban 2020 da ƙungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu ta Najeriya IPMAN, ta umarci ‘ya’yanta su ƙara kuɗin farashin mai zuwa Naira 162 kan kowace lita.

Karin ya biyo bayan sanarwar da hukumomin Najeriya suka yi na kara kudin mai zuwa N151.56k.

Tushen Labari

Karin Wasu

Sababbin Wallafa