Connect with us

Featured

Gwamnatin Najeriya ta Gargadi Shafin Facebook – DFOnline

Published

on

Shafin Facebook

Gwamnatin Najeriya ta Gargadi Shafin Facebook da sauran shafukan sada zumunta.

Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya buƙaci shafin Facebook da sauran shafukan sada zumunta da su daina barin ƴan ƙungiyar IPOB da ke fafutikar kafa ƙasar Biafra su na amfani da shafin wurin neman tayar da zaune tsaye ko kuma haɗa rikicin ƙabilanci.

Ministan ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Talata bayan wata tattaunawa da ya yi tare da wakilan kamfanin Facebook.

Lai Mohammed ya bayyana cewa tun da gwamnatin tarayya ta ayyana IPOB a matsayin ƴan ta’adda, Shafin Facebook ba shi da hurumin ba ‘yan IPOB damar bayyana ra’ayinsu.

Ministan ya bayyana cewa duk da an dade ana ta ƙorafi ga Facebook kan ayyukan ‘ƴan IPOB, amma kamfanin bai yi komai ba wajan dakatar da su.

Ya ƙara da cewa a yanzu gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da sanya idanu akan Shafin Facebook da sauran shafukan sada zumunta a ‘ƴan kwanakin nan domin tabbatar da cewa sun bi ƙa’idoji.

Tushen Labari

Duniyar Fasaha Online – #Gwamnatin #Najeriya #Gargadi #Shafin #Facebook

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku