Connect with us

Fasaha

Hanyar magance kutse a shafin intanet

Published

on

hanyar tsaro 2fa

Hanyar da za a magance kutse a shafin intanet

Sanin kowane musamman ga masu mu’amala da shafukan intanet, cewa aiyukan kutse sun ta’azzara musamman a shafukan zumunta, akwatin aikawa da karbar sakonni (na email), shafukan hadahadar cinikayya da sauran shafuka masu muhimmanci wajan gudanar da harkoki a rayuwar Jama’a.

A kwanakin baya bayan nan na sami korafe korafe daga Mutane masu yawa akan cewa anyi kutse ko ankwace musu ragamar kulawa da sarrafa shafukan su. Musamman shafukan zumunta na Facebook da Instagram. Wadanda har kudi suke kashewa wajan neman a dawo musu da account din su.

Da farko na kan dora alhakin faruwar haka akan masu shafuka ko account a intanet. Saboda sakacin amfani da password mara sarkakiya, sukan yi amfani da sunayensu ko lambobin waya don gudun mantuwa, haka kuma sukanyi amfani da password guda daya a dukkanin shafukan su na intanet. A wasu lokutan ma sukan yi amfani da na’urorin da banasu ba wajan bude shafukan su, domin yin mu’amalar da suka saba a intanet.

Idan mutum yayi amfani da kwamfuta ko wayar da ba mallakinsa ba, to idan ya kammala aiki da ita, yanada kyau yayi logout ko signout, sannan ya goge bayannan sirrin aiyukan (browsing history) da ya aiwatar daga manhajar browser da yayi amfani da ita. Haka kuma yanada matukar muhimmanci mutum ya kirkiri password mai karfi wadda baza a iya ‘yar canke (guess) akan ta ba. Misalin password mai karfi;

  • Ana so ta kasance haruffa da lambobi har ma da alamomi
  • Kuma ta kasance mai tsaho kamar kwaya 10 -12 koma fiye da haka
  • Sannan kuma ta kasance an cakuda manyan bakake da kananan bakake wajan rubuta haruffan

Misali: Abc123FG$#? da kuma ?/@jklW456 da sauran su…

password-lambobin-tsaro

Amma a duk lokacin da akayi amfani da suna ko kalmar turanci a matsayin password to akan gamu da matsaloli. Sannan Jama’a suna da sakaci wajan ziyartar/duba akwatunan sakonnin su (email). Ma’ana basa dubawa akai-akai. Saboda a lokacin da ake kokarin yi maka kutse akwai manhajar dake lura da tsarin yadda kuke ziyartar shafukan ku a lokuta da yawa har ta gane ku. To idan ta ga sabon tsarin da yasha bamban da yadda kuka saba, zata aika da sako gare ku ta email. Haka zai baku zabi cewa idan kaine kake korin shiga ta wata siga, to ka manta da sakon, idan kuma ba kai bane to kayi gaggawar daukar mataki akan lokaci. Haka zalika idan baza ku iya da kanku ba to zasu yi guiding dinku daki-daki.

Amma fa, shi kansa sakon ya kamata ayi hattara, a kula da kyau kada a fada komar hakas. A tabbatar da sahihanci da asalin tushen sakon kafin daukar mataki. A daidai wannan gabar nake so na bayyana hanyar kara matakin tsaro ga dukkan shafuka ko account na intanet.

Two Factor Authentication (2FA)

Hanya ce mai saukin aiwatarwa, wadda take kara karfin matakan tsaro a shafukan intanet. An kirkiro wannan hanya ne domin dakile ko toshe aiyukan ‘yan ta’addan intanet (hackers). Haka zalika tsarin yakan tantance ne ta hanyar aika sakon lambobin sirri zuwa wayoyin ku (lambobi kwaya 6) bayan kun saka Username da Password, sannan ku shigar da lambobin a gurbin da aka tanada domin tantacewa.

fasahar tsaro ta 2fa

A halin yanzu wannan hanya itace kan gaba wajan bada tsaro a shafukan intanet. Kuma dukkanin manhajoji kamar na bankuna da sauran su, da ake amfani da su akwai wannan fasahar tsaro ta 2FA.

Mu hadu a rubutu na gaba akan yadda ake kunna su…