Connect with us

Fasaha

Hanyoyi 5 da za ku gane tsarin zuba jari na bogi

Published

on

Hanyoyi 5 da za ku gane tsarin zuba jari na bogi

Tsarin zuba jari na ban-biyar-in-ba-ka-goma wani salon zuba jari ne na bogi inda ake yi wa mai zubawar alƙawarin samun riba mai tsoka cikin ƙanƙanin lokaci.

A wannan tsarin, waɗanda suka kafa ‘kamfanin’ zuba jarin na yaudarar mutane ne ta hanyar ba su riba mai tsoka daga farko sannan su ce su kawo ƙarin mutane su shiga tsarin don ruɓanya masu ribarsu ta gaba.

Wani lokaci, masu yaudarar kan yi amfani da wata haja su ce idan ka siyar da adadi kaza kuma ka yi wa mutum kaza rajista a ƙarƙashinka za ka samu wasu maƙudan kuɗi.

A Najeriya, wannan tsarin ya samu wurin zama ba tun yau ba.

An samu kamfanoni da dama da ke iƙirarin na zuba jari ne ko kuma su ce suna ruɓanya wa mutum kuɗi cikin wata guda ko wata uku ko shida.

Wasu kuma kan ce idan mutum ya zuba kuɗinsa a kamfaninsu, zai samu sau goman abin da ya sa ko ma fiye a cikin shekara guda.

Ko a shekarun baya-bayan nan, ƴan Najeriya da dama sun faɗa tarkon wani babban kamfanin da ke tsarin zuba jari irin wannan mai suna MMM kuma dubban mutane sun yi asarar miliyoyi.

Rana guda mutanen da suka zuba jari a MMM suka wayi gari kamfanin ya tsayar da ayyukansa cik ba tare da biyan mutane maƙudan kuɗin da suka zuba a cikinsa ba.

Kusan a iya cewa kullum cikin samun kafuwar irin waɗannan kamfanonin ake yi.

Hukumar da ke kula da hannayen jari ta ƙasa, SEC ta sha fitar da sanarwa da gargaɗi ga ƴan ƙasar kan irin waɗannan kanfanonin.

Sufian Abdulkarim na hukumar SEC ya ce duk da wannan gargaɗi da hukumarsa ke fitarwa ƴan Najeriya na ci gaba da zuba kudadensu da zarar wani ya ɓullo.

Sai dai ya bayyana hanyoyin da za a iya saurin gane irin kamfanonin da ke tsarin na zuba jari na ban-biyar-in-ba-ka-goma:

Alƙawarin samun riba mai tsoka cikin ƙanƙanin lokaci

Mista Sufian ya ce abu na farko da ya kamata mutane su yi la’akari da shi, shi ne a duk inda aka zuba jari a kan ɗauki tsawon lokaci kafin a fara samun ribar ƙudin da aka zuba.

“Amma sau da yawa kamfanonin na ƙarya kan ce wa mutane za su mayar da kuɗinsu har ma da riba cikin ɗan ƙaramin lokaci.

“Kuma ba lallai ma masu kamfanin su sanar da mai zuba jarin irin sana’ar da za su yi su juya masa kuɗinsa ba,” a cewarsa.

Mista Sufian ya ce babu zuba jarin da babu hatsari a cikinsa, ma’ana ana iya samun riba ko a faɗi.

“Amma masu wannan tsarin kan tabbatar wa mutane cewa ba a faɗuwa kwata-kwata a nasu shirin,” in ji shi.

“Da ka ga irin haka, lallai ka tsaya ka sake bincike kafin ka miƙa masu kuɗinka,” a cewar Mista Sufian.

Haka kuma, su kan yi hayar mutane su riƙa nuna cewa sun zuba jari a kamfanin kuma suka mayar da kuɗinsu ninkin-ba-ninkin.

Wani lokaci su kan wallafa hotuna da labarin wadanann mutanen na ƙarya a shafukansu na inatnet.

Wasu kan nuna sun sayi gidaje da motoci a ciki da wajen Najeriya duk da ribar da suka samu daga kamfanin.

Wannan kan yi saurin jan ra’ayin mutane musamma idan suka gan su fes ko a mota mai tsada.

Babu sunan kamfanin a jerin kamfanonin da hukumar SEC ke bugawa a shafinta

Mista Suffian ya ce duk wani kamfani zuba jari na ainihi ya yi rajista da hukumar SEC kuma ta na buga sunayensu a shafin ta na sec.gov.ng

“Wannan ce hanya mafi sauƙi da mutum zai tabbatar da inda yake zuba kuɗinsa.

Idan babu sunan kamfanin a shafinmu na inatnet to kamfanin na bogi ne,” in ji shi.

Masu kamfanin ba su gaya maka ainihin sana’ar da suke yi su juya kuɗinka ba

Sau da yawa masu tsarin zuba jari na zuba jari na ban-biyar-in-ba-ka-goma ba sa bayyana irin sana’ar da suke yi.

Su kan gaya wa masu zuba jari cewar hedikwatar kamfaninsu na can a wata ƙasa a Turai ko a nahiyar Asiya kuma a nan ne ake sarrafa kuɗin.

Wasu daga cikinsu ma kan buga fasta ɗauke da hotunan turawa a ofisoshi su yi ta rabawa mutane.

Haka kuma, ko mai zuba jari ya nemi ƙarin bayani, su kan ce masa ba zai fahimta ba ko kuma su yi masa wani bayani da zai ɓatar da shi.

Duka wannan salon yaudara ne a cewar Mista Sufian.

Haka kuma su kan nuna wa mai zuba jari idan ya zuba kuɗi masu yawa, zai fi samun riba cikin gaggawa.

Su kan yi hakan ne don su samu masu zuba jarin da dama cikin sauri.

Masu kamfanin za su matsa ka samo ƙarin masu zuba jari

Irin waɗannan tsare-tsaren sun dogara ne da sabbin mutane da za su kawo kuɗinsu.

Wannan ne zai ba su damar biyan riba ga mutanen da suka zuba jari daga farko-farko.

Su kuma waɗannan mutane za su ƙara amincewa da sahihancin kamfanin har su ƙara zuba wasu kuɗin sannan su jawo ra’ayin ƴan uwa da abokai su ma su sa kuɗinsu.

“Wani salo ne da suke amfani da shi. Wannan kuɗin na farko da muatne suka yi ta tururuwar zubawa, su za su yi amfani da su wajen biyan wasu a matsayin jari.

Suna yin wannan kuma suna matsawa kwastomominsu su kawo ƙarin mutane su zuba jari.

To idan wanda suka zuba daga farko suka yi sa’a kuɗinsu ya fita, wanda za su zo daga baya na cikin hatsari,” a cewar Sufian.

Don kuwa ya ce watakil ka zuba kuɗinka masu yawa da wata ɗaya ko biyu kuma an yi maka alƙawarin karɓar uwar kuɗinka da riba cikin wata uku amma ranar da za ka karɓa kana zuwa ofishinsu sai ka ga sun tashi.

“Na ga mutane da yawa da irin haka ta faru da su,” a cewarsa.

Babu takardu da za a sa hannu a kai

A duk lokacin da za a zuba jari bisa ƙa’ida, dole ne mai zubawar da wanda ake zuba wa su sa hannu kan yarjejeniya.

Sai dai a irin tsarin ban-biyar-in-ba-ka-goma da wuya a sa hannu kan wata yarjejeniya.

Asali ma a titi a ke haɗuwa da wakilan kamfanonin ko kuma a ga tallukansu a shafukan sada zumunta.

Nan take kuma su ce sun yi wa mutum rajista sannan a yi masa bayanin yadda zai zuba kuɗin.

Mista Sufian ya ce wannan ma wata babbar alama ce ta babu ƙamshin gaskiya a lamarin.

“Mafi yawansu ba wani ofis ne da su ba, wataƙil ɗan shago ne ma amma da yake za su ce hedikwatarsu na can Turai sai masu zuba jari su yarda,” a cewarsa.

Me ya sa mutane ke shiga wannan tsarin?

Mista Sufian ya ce a Najeriya a iya cewa talauci ne ke sa mutane amincewa da irin wannan tsarin.

“Ga matasa da dama a ƙasar da suka yi karatu amma ba aikin yi. Manufofin gwamnati ba su duba waɗannan matasa.

“Shi ya sa da zarar sun ji hanyar samun kudi su ke tururuwar zuwa. Kana zaune an ce ka kawo dubu goma cikin mako guda za a ba ka ribar dubu hamsin, me zai hana ba za ka ba?” in ji shi.

Sannan ya ce babu wasu dokoki masu ƙwari da ke yaƙi da kamfanonin na bogi.

Sai dai ya ce hukumarsa ta SEC da wasu ɓangarorin gwamnati kamar Babban Bankin Ƙasar da Rundunar Ƴan sanda da Hukumae EFCC da sauransu sun hada wajen samar da wani shiri da za a dakushe waɗanann kamfanonin.

“Kullum ana cikin kama su kuma kullum ana samun sabbi masu tasowa, don haka dole sai an haɗa kai an yi maganinsu,” a cewar Mista Sufian.

Ya kuma ce dole a riƙa wayar wa mutane da kai su fahimci hanyoyin da za su gane tsarin zuba jari na bogi.

“Kusan ko yaushe muna fitar da sanarwa da gargaɗi kan wannan amma mutane ba sa ji.

“Rashin sani ne da rashin ilimi ke jefa mutane cikin irin wannan halin. Idan aka riƙa wayar wa mutane da kai sa a samu sauki,” in ji Sufian.

Tushen Labari

Continue Reading
Click to comment

Ku Fadi Ra'ayin Ku